Dalilin Da Ya Sa Ban Rika Tsoma Baki Ba a Harkokin Majalisa Ba a Tsawon Mulkina, Buhari Ya Yi Bayani

Dalilin Da Ya Sa Ban Rika Tsoma Baki Ba a Harkokin Majalisa Ba a Tsawon Mulkina, Buhari Ya Yi Bayani

  • Shugaba Buhari ya ce duk tsawon shekaru takwas da gwamnatinsa ta yi, bai yi katsalandan a harkokin majalisar kasar ba saboda ya san cewa majalisa cin gashin kanta take
  • Buhari ya danganta nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kyakkyawar alaka tsakanin bangaren shugabanci da na majalisa
  • Buhari ya ce majalisa ita ce ginshikin dimokuradiyya kuma tana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ganin an yi la’akari da muradan ‘yan Najeriya a yayin kafa sabuwar doka

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce bai taɓa yin katsalandan a harkokin majalisar Najeriya ba tsawon shekaru takwas da ya kwashe yana mulki.

Buhari ya ce ya yi hakan ne saboda ya yi amanna da cewa majalisar zaman kanta ta ke yi, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai rika tsoma baki ba a harkokokin majalisa
Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai rika tsoma baki ba a harkokokin majalisa. Hoto: Leadership
Asali: UGC

Kyakkyawar alaƙa da majalisa ne silar nasarorin da muka samu

Shugaban ya kuma alaƙanta nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kyakkyawar alaƙa da aka samu tsakanin bangaren shuwagabanni da kuma na majalisa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da yake ƙaddamar da mazauni na dindindin na cibiyar nazarin majalisu da dimokuraɗiyya ta ƙasa (NILDS) a Abuja ranar Alhamis.

Buhari ya ce ya na fatan cibiyar za ta ƙara taimakawa wajen ɗaga darajar majalisa a Najeriya da ma Afrika baki ɗaya.

Ya ce:

"Kamar yadda kuka sani, na zagaya sassan Najeriya a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, inda na ƙaddamar da wasu muhimman ababe na more rayuwa na ƙasa waɗanda gwamnatina ta kammala a cikin shekaru takwas da suka gabata."
“Nasarorin da muka samu sun samo asali ne daga kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin bangaren shugabanni da na majalisu.”

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Buhari ya ƙara da cewa majalisa itace ginshikin tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya, saboda ita ce ke kula da irin buƙatun al'umma a yayin kafa sabbin dokoki.

Sannan Vanguard ta kawo Buhari na cewa majalisa ce ke sanya idanu kan shugabanni domin tabbatar da cewa suna kashe kuɗaɗen gwamnati a bisa manufofin da aka tsara.

Na yi fafutukar ganin majalisa ta samu damar cin gashin kanta

Buhari ya kuma ƙara da cewar tun lokacin da aka zaɓesa a 2015 ya yi fafutukar ganin an bai wa majalisa damar cin gashin kanta ta yadda zata iya zaɓar shugabanninta ba tare da an sanya mata baki ba.

Buhari ya ƙara da cewar baya tsoma baki a harkokin majalisa. Ya ce ya ma yi ƙoƙarin ƙulla kyakkyawar dangantaka tsakanin ɓangarorin gwamnati da na majalisar.

Buhari ya kuma bayyana cewa abubuwa da dama da aka samu na ci-gaba a ƙasar nan, na da nasaba da irin kyakkyawar dangantaka da ke tsakaninsa da majalisa.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Gwamntin Buhari za ta ci-gaba da karbo bashi har zuwa 29 ga Mayu.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta daina kwangiloli da ciyo bashi ba har sai zuwa 29 ga watan Mayu.

Babatunde fashola ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnatin Buhari ba za ta daina bada kwangila da ciyo bashi ba har sai daren 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng