Gwamna Ortom Ya Debo da Zafi, Ya Tona Masu Cin Hanci a Fadar Shugaban Kasa

Gwamna Ortom Ya Debo da Zafi, Ya Tona Masu Cin Hanci a Fadar Shugaban Kasa

  • Gwamna Ortom ya ce cin hanci da rashawa ya samu gindin zama a fadar shugaban kasa lokacin mulkin Buhari
  • Ortom ya kuma ɗora laifin faɗuwar da ya yi a zaben Sanata kan wasu a cikin fadar kujera lamba ɗaya a Najeriya
  • Ya kuma nuna adawarsa ƙarara da shirin shugaba Buhari na guduwa zuwa jamhuriyar Nijar idan aka matsa masa

Benue - Gwamnan jihar Benuwai mai barin gado, Samuel Ortom, ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa sun yi katutu a fadar shugaban ƙasa, Aso Billa.

Gwamna Ortom, wanda ya sha kaye a zaben Sanata a 2023, ya faɗi haka ne yayin zantawa da kafar watsa labarai Arise TV ranar Laraba.

Gwamna Samuel Ortom.
Gwamna Ortom Ya Debo da Zafi, Ya Tona Masu Cin Hanci a Fadar Shugaban Kasa Hoto: Samuel Ortom
Asali: UGC

Gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa ce ta kulla makirce-makircen da suka sa ya sha ƙasa a zaben Sanatan da ya nema, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Ortom, wanda ya ce ya hakura kuma komai ya wuce, ya yi ikirarin cewa mutanen cikin Villa ba su ƙaunarsa, "Sabida suna tunanin ina kawo musu cikas a tafiyar da harkokinsu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, gwamna Ortom ya ce:

"Yadda aka yi murnar faɗuwar da na yi ya nuna dama daga Villa aka ƙulla makircin ganin baya na ta kowane hali. Sun kashe makudan kudaɗe domin dakatar da ni."
"Mutane na yawan magana kan cin hanci da rashawa amma asalin cin hanci na cikin Villa. Na san zunzurutun kuɗin da fadar shugaban ƙasa (Villa) ta turo jihar Benuwai don kawai a kayar da ni zaɓe."
"Shikenan na faɗi zaɓe, na san haka Allah ya tsara kuma na rungumi kaddara, na yarda. Suna tunanin na tsare musu hanya ne amma ba haka lamarin yake ba, buri na a yi adalci da daidaito."

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Gwamna Ortom ya soki aniyar shugaba Muhamamdu Buhari na guduwa zuwa Nijar, idan aka ƙuntata masa a Najeriya, ya buƙaci ya tsaya ya goyi bayan sabuwar gwamnati.

"Ba Zan Kunyata Yan Najeriya Ba," Bola Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

A wani labarin kuma Bola Tinubu ya sha alwashin cewa ba zai kunyata 'yan Najeriya bisa amanar da suka ɗora masa ba.

Zababben shugaban ƙasan, wanda zai hau gadon mulki nan da yan kwanaki, ya ce ya fahimci girman aikin da ke gabansa da kuma tsammanin da ake wa gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel