Atiku Zai Karbi Najeriya Daga Hannun Tinubu Cikin Wata 6, Bwala

Atiku Zai Karbi Najeriya Daga Hannun Tinubu Cikin Wata 6, Bwala

  • Kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na PDP, Daniel Bwala, ya ce Tinubu ba zai wuce wata 7 a kan madafun iko ba
  • A cewarsa, bayan nan za'a sauke shi daga kan kujerar shugaban ƙasa a ɗora Atiku Abubakar na jam'iyar PDP
  • Ya ce PDP ta yarda cewa ta tafka kura-kurai a Najeriya amma ta nemi yan ƙasa su yi hakuri su ƙara ba ta dama

Mamban jam'iyyar PDP kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya ce PDP zata karɓe mulki daga hannun zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Mista Bwala ya bayyana cewa PDP zata kwace mulki hannun Bola Tinubu watanni shida bayan rantsarwa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Bwala da Tinubu.
Atiku Zai Karbi Najeriya Daga Hannun Tinubu Cikin Wata 6, Bwala Hoto: Bwala Daniel, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Babbar jam'iyyar adawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa sun kalubalanci matakin INEC na ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"Ban Gane Ba," Atiku Ya Maida Martani Kan Kiran da Sakataren Amurka Ya Yi Wa Tinubu Ta Wayar Tarho

A ƙarar da suka shigar gaban Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban kasa sun jera INEC, Tinubu da jam'iyyar APC a matsayin waɗanda suke tuhuma na 1 da na 2 da na 3 bi da bi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, Kotu zata ci gaba da sauraron ƙarar Atiku da PDP.

PDP ta gane kuskurenta, ta nemi afuwar yan Najeriya

Da yake zantawa da Arise TV kan karar, an nemi Daniel Bwala ya yi karin haske kan ikirarin jam'iyyar APC cewa a tarihi babu jam'iyyar da ta yi ƙaurin suna wajen maguɗin zaɓe kamar PDP.

A kalamansa ya ce:

"Tun da daɗewa a shekarun da suka gabata PDP ta aminta cewa ta tafka kura-kurai a zamanin mulkinta. Zan iya tuna cewa lokacin da Secondus ya zama shugaban jam'iyya ya ba da hakuri."

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Kuskure: An Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

"Ya jagoranci kamfe a sassan Najeriya yana faɗa wa yan ƙasa cewa PDP ta gane kuskurenta su yi hakuri su yafe mata. Ƙa taba jin APC ta nemi yafiya?"

Yadda zamu kwace mulki bayan wata 6 - Bwala

Dangane da kwarin guiwarsa kan ƙarar da PDP ta kai gaban Kotu, Mista Bwala, ya ce Tinubu zai hau gadon mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023 amma watanni 6 ƙaɗai zai shafe.

A cewarsa bayan waɗan nan watanni, Kotu zata tsige shi daga kujerar shugaban ƙasa ta maye gurbinsa da Atiku na jam'iyyar PDP.

"Idan (Tinubu) ya karbi mulki ranar 29 ga watan Mayu, watanni 6 zuwa 7 zai kwashe kan madafun iko kafin a sauke shi, daga nan zamu zo mu karbi haƙƙinmu."

APC ta yi kuskure da ta baiwa Tinubu takara

A wani labarin kun ji cewa Peter Obi Ya Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

Kara karanta wannan

Goro a Miya: Wasu Shugabannin APC Sun Kebe da Makiyin Tinubu, Tsohon Shugaba a PDP

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP ya ce sai da ya faɗa wa jam'iyya mai mulki wanda ya cancanci ta baiwa tikitin takarar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel