Rikicin Jam'iyya: An Dakatar Da Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa? NWC Ta Yi Bayani Kan Hukuncin

Rikicin Jam'iyya: An Dakatar Da Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa? NWC Ta Yi Bayani Kan Hukuncin

  • Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa dakatawar da aka yi wa tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ahmed Markafi a matsayin aikin banza
  • Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar ta PDP ne ya bayyana hakan, sannan kuma ya bayyana cewa 'yan jam'iyyar na Tudun Wada da suka sanar da dakatarwar ba su bi kundin PDP ba
  • Shugaban jam’iyyar PDP na Tudun Wada Kaduna, Saidu Aliyu ne ya sanar da dakatarwar a ranar Lahadi

FCT, Abuja - An bayyana dakatarwar da aka yi wa Ahmed Makarfi, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, a matsayin aikin banza.

A wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, kwamitin ayyuka na ƙasa na jam’iyyar ne ya sanar da janye dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu.

Makarfi/PDP/Rikicin Jam'iyya
PDP ta janye dakatarwar da aka yi wa tsohon shugabanta, Ahmed Makarfi. Hoto: PDP Update
Asali: Twitter

Ana zargin Maƙarfi da cin amanar jam'iyya

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Ta Karrama Gwamnonin PDP, Ciki Har da Gwamna Wiki da Wasu 2 Na G-5

Tun a ranar Lahadi, 14 ga watan Mayu, wakilan Tudun Wada na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna suka sanar da dakatar da Makarfi bisa zargin cin amanar jam’iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saidu Aliyu, shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Tutun-Wada, da wasu mutane 5 ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar.

Sun zargi Makarfi da nuna son kansa da kuma rashin haƙuri da ra’ayoyin jama'a, inda suka ƙara da cewa yana aikata ayyukan cin amanar jam'iyya.

Dakatarwar ba ta da wani tasiri

Amma da yake mayar da martani kan wannan mataki a ranar Litinin, Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar PDP, a wata sanarwa, ya ce dakatarwar ba ta da wani tasiri.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Bayan nazarin da kwamitin aikace-aikace ya yi, kan batutuwan da wakilan jam'iyya na gundumar Tudun Wada suka gabatar, gami da kuma irin matakin da suka ɗauka, wanda ya shafi abubuwan da suke da alaƙa da ladabtarwa, ina mai shaida muku wannan mataki bai yi ba, kuma ba shi da. wani tasiri."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Sanar Da Yin Azumi Na Kwana 7 Don Samun Nasara a Kotu

Matakin ya saɓa da dokokin jam'iyyar PDP

Ologunagba ya ci gaba da cewa, hukuncin da wakilan gundumar suka yanke bai dace da tanadin kundin tsarin jam'iyyar PDP ba, kamar yadda aka gyara shi a shekarar 2017.

Daga nan kwamitin ya yi kira ga haɗin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar musamman a wannan lokaci da ake samun rarrabuwar kawuna.

Kotu ta hana NYSC yin magana kan gwamnan PDP

A baya Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja da ta haramtawa hukumar NYSC yin tsokaci game da Peter Mbah, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Enugu.

Lauyan zaɓaɓɓen gwamnan, Emeka Ozoani (SAN) ne ya shigar da ƙara inda ya ɓuƙaci kotu ta bayyana matsayin doka kan matakin da ya dace da hukumar NYSC da daraktan bayar da shaidar kammala yi wa ƙasa hidima, Ibrahim Muhammad.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel