APC Ta Tabbatar da Dakatarwar da Aka Yi wa Sanata, Minista da Kusoshin Jam’iyya

APC Ta Tabbatar da Dakatarwar da Aka Yi wa Sanata, Minista da Kusoshin Jam’iyya

  • Jam’iyyar APC na reshen Kudu maso gabas ta ladabta wasu ‘ya ‘yanta daga jihohin Abia da Enugu
  • Ministan harkokin kasar waje da tsohon shugaban majalisar dattawa su na cikin wadanda aka hukunta
  • Kafin nan shugabannin reshe sun zauna a kan ‘yan siyasar, sun zarge su da yi wa APC makarkashiya

Abuja - APC na bangaren Kudu maso gabas ya tabbatar da matakin dakatarwar da aka dauka kan wasu ‘ya ‘yan jam’iyya a jihohin Enugu da Abia.

A ranar Alhamis Vanguard ta kawo rahoto cewa shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun yi zama a kan dakatar da wasu da aka yi a kwanaki.

Shugaban APC na bangaren kudu maso gabas, Dr. Ijeomah Arodiogbu ya ce ya zama dole a rika ladabtar da duk wani ‘dan jam’iyya da aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Samu Goyon Bayan Na Kusa da Shugaba Buhari a Zaben Majalisa

"A wannan gaba, shiyyar Kudu maso gabas ta karbi jerin sunayen wadanda shugabannin reshen jihohin Abia da Enugu na APC su ka dakatar da su.
An samu wadanda aka dakatar da laifin yi wa jam’iyya makarkashiya a mazabunsu, sai shugabannin APC na shiyya suka tabbatar da hukuncin.
'Yan APC
Magoya bayan APC Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran wadanda aka dakatar

Daga cikinsu akwai tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, tsohon Gwamna, Sullivan Chime.
Akwai tsohon shugaban majalisar dokokin Enugu, Hon Eugene Odo, tsohon Kwamishina a jihar, Joe Mmammel da shugaban VOA, Osita Okechukwu.
Tsohon Gwamnan soja, Joe Orji, Mr. Maduka Arum (wanda aka fi sani da Mama) da kuma wasunsu.

- Jam'iyyar APC

Sahara Reporters ta ce daga Abia, an tabbatar da dakatarwar da aka yi Orji Uzor Kalu, Hon Sam Nkeire, Hon. Uche Sampson Ogah da Nkechi Nworgu.

Kara karanta wannan

Zababbun Sanatocin APC 2 Su na Rububi a Kan Kuri’un ‘Yan PDP a Majalisar Dattawa

Sakataren yada labaran APC na reshen Enugu, Cif Ezeanyawu Michael ya ce matakin da aka dauka ya yi daidai, ya bada shawara a ladabta masu laifin.

Bayan an yi bincike, an dakatar da Hadimin Ministan harkokin waje, Flavour Eze, tsohon shugaban jam’iyyar APC, Ben Nwoye da kum Chidera Obed.

Prince Adewole Adebayo ya sallama

Rahoto ya zo cewa 'dan takaran SDP a zaben shugaban kasa, Mista Prince Adewole Adebayo bai da niyyar ja da Bola Tinubu game da takarar 2023.

Duk da APC ta doke shi a 2023 kuma yana ganin Tinubu sun yi magudi, hakan ba zai jawo ya tafi kotu ba, ya ce a ba gwamnati mai zuwa hadin-kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel