Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: Gwamna Wike Ya Ayyana Ranar Laraba Matsayin Ranar Hutu

Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: Gwamna Wike Ya Ayyana Ranar Laraba Matsayin Ranar Hutu

  • Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ayyana ranar hutu a jihar domin tarbar Bola Tinubu
  • Wike ya bayyana ranar Laraba matsayin ranar hutu a jihar domin tarbar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar
  • Bola Tinubu zai ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin Wike ta aiwatar a jihar

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ayyana ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023, a matsayin ranar hutu a jihar domin ziyarar da Bola Tinubu zai kai a jihar.

Channels tv tace wani saƙo da ya aikewa mutanen jihar, gwamna Wike, ya ce Tinubu zai ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar cikin kwanaki biyu, ranar Laraba da Alhamis.

Gwamna ya bayyana ranar Laraba matsayin ranar hutu a Rivers
Gwamna Wike da Bola Tinubu a yayin wata ziyara Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Ya lissafo ayyukan da suka haɗa da gadar sama ta Rumuokwuta-Rumuola da sabuwar harabar kotun majistare a ƙananan hukumomin Obio/Akpor da Port Harcourt na jihar.

Kara karanta wannan

To Fa: Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Ƙara Shiga Sabon Tasku Kan Ayyana Aishatu Binani

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wajen mu wannan abin alfahari ne ga gwamnati da mutanen Rivers mu ƙarbi baƙuncin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a wannan ziyarar mai ɗumbin tarihi."
"A dalilin hakan, ina kira ga dukkanin mutanen jihar Rivers da su fito kwansu da ƙwarƙwatar su, su tarbi zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mu, mai girma Sanata Bola Ahmed Tinubu, sannan su nuna al'adar Rivers ta mutunta baƙi, yayin da ya ƙaddamar da waɗannan ayyukan cigaban."

Gwamnan ya kuma bayar da umurnin dukkanin wasu shaguna da wuraren kasuwanci a kan titin Rumuokwuta-Rumuola, da su kasance a kulle daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana lokacin da za a ƙaddamar da gadar saman.

"A bisa hakan, na ayyana ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023, a matsayin ranar hutu, domin ba mutanen jihar Rivers damar tarbar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mu." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Kara Ɗage Kidayar 2023 da Aka Shiya Yi a Najeriya

Gwamnan ya kuma buƙaci ƴan kasuwa da ƙungiyoyin ma'aikata da su fahimce shi da idon basira kan wannan hukuncim da ya yanke, cewar rahoton Vanguard.

Kungiyar Mayu Da Matsafa Ta Bukaci Yan Najeriya Su Yi Wa Tinubu Addu'a

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa ƙungiyar mayu da matsafa ta buƙaci ƴan Najeriya da su sanya Bola Tinubu, a cikin addu'a.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne, gabanin a rantsar da Bola Tinubu, a kujerar shugabancin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel