Shugaba Buhari Ya Sake Daga Kidayar Mutane da Gidaje a Najeriya

Shugaba Buhari Ya Sake Daga Kidayar Mutane da Gidaje a Najeriya

  • A karo na biyu, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ɗage kidayar 2023 da aka shirya gudanarwa a Najeriya
  • Ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da shugaban NPC na ƙasa, Nasir Isa-Kwarra, da tawagarsa a fadar shugaban ƙasa
  • A halin yanzun, Buhari ya bar wuƙa da nama hannun gwamnati mai zuwa karƙaashin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sake ɗaga aiki kidayar mutane da gidaje a Najeriya na shekarar 2023.

Jaridar ta ce shugaban ƙasan ya ɗage aikin kidayar wanda aka tsara gudanarwa ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayu, 2023, a yanzu ya bar wuƙa da nama hannun sabuwar gwamnati.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Sake Daga Kidayar Mutane da Gidaje a Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya ɗauki wannan matakin ne a wurin ganawa da wasu mambobin majalisar zartaswa da shugaban hukumar kidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Isa-Kwarra, da tawagarsa a Abuja ranar Jummu'a.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa Tinubu, Hotuna Sun Bayyana

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai da safiyar Asabar mai ɗauke da sa hannun Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta ce:

"Yayin da aka cimma matsayar sake ɗage aikin kidayar, taron ya kara jaddada muhimmancin kidayar yan Najeriya da gidaje, shekaru 17 bayan gudanar da kidaya a Najeriya."
"Hakan ne kaɗai zai sa a tattara bayanai waɗanda zasu taimaka wajen cika burin kawo ci gaba a ƙasar nan kuma ya daidaita walwaha a rayuwar mazauna Najeriya."

A wurin taron, an ji shugaba Muhammadu Buhari na cewa an cimma nasarori masu yawa a shirye-shiryen gudanar da kidaya, wacce aka ɗaga yanzu.

Ya kuma yaba wa hukumar kidaya ta ƙasa NPC bisa yadda ta ɗauki tsaruka da hanyoyin gudanar da sahihiyar kidaya wacce za'a dogara da ita a gwamnatance.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Daɗe a Daura Ba" Shugaba Buhari Ya Canja Garin da Zai Koma Bayan Miƙa Mulki Ga Tinubu

Jiga-jigan da suka halarci zaman

Manyan kusoshin gwamnati da suka je wurin taron sun kunshi, Antoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed.

Sauran su ne, ƙaramin ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Mista Clem Agba, da kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnonin PDP sun gana da Tinubu a Abuja

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Gana da Tinubu a Abuja, Ya Fadi Kalamai Masu Jan Hankali

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun ziyarci shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Bayan ganawarsu, gwamna Wike ya ce siyasa ta ƙare, ya kamata ko wane ɗan Najeriya ya baiwa sabuwar gwamnati goyon bayan da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel