Jerin Yan Takarar Gwamna a Inuwar APC, PDP da Labour Partya a Bayelsa

Jerin Yan Takarar Gwamna a Inuwar APC, PDP da Labour Partya a Bayelsa

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa zata gudanar da zaben gwamna a jihar Bayelsa ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Yayin da zaɓen ke ƙara matsowa, ana ganin zaben zai kwashi yan kallo tsakanin yan takarar manyan jam'iyyun siyasa uku a Najeriya, jam'iyyar APC, PDP da kuma Labour Party.

Nan da ranar 11 ga watan Nuwamba, INEC zata gudanar da zaben gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi, waɗanda zabensu ke gudanar ba'a lokacin babban zaɓe ba.

Manyan yan takara a Bayelsa.
Jerin Yan Takarar Gwamna a Inuwar APC, PDP da Labour Partya a Bayelsa Hoto: Douye Diri, Timipre Marlin Sylva
Asali: Facebook

A wannan shafin, Legit.ng Hausa zata haska muku 'yan takarar gwamna a inuwar manyan jam'iyyu da ke hangen zama kujera lamba ɗaya a jihar Bayelsa.

1. Timipre Sylva na jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Dakta Timipre Sylva, zai tunkari zaɓen gwamna ne da fatan sake komawa gidan gwamnati da ke Yenagoa.

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: INEC Ta Baiwa Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa Shaidar Samun Nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sylva, tsohon ƙaramin ministan Albarkatun Man Fetur a wannan gwamnati mai ci karkashin shugaba Muhammadu Buhari, ya rike gwamnan Bayelsa tsakanin 2008 zuwa 2012.

Babu tantama ɗan takarar da APC ta kai sunansa ga INEC, Sylva zai iya kawo cikas ga kokarin tazarcen gwamna mai ci duba da gogewarsa da kwarewa a kan harkar shugabanci.

2. Udengs Eradiri na Labour Party

Ɗan takarar gwamna da jam'iyyar Labour Party ta tsayar a zaben gwamnan jihar Bayelsa mai zuwa shi ne Udengs Eradiri.

Masana da masu sharhi kan siyasa suna ganin cewa damar Eradiri ta lashe zaben gwamnan ɗan taƙi ne kuma ba ƙaramin abin al'ajabi bane ya kai labari a zaɓe mai zuwa.

3. Douye Diri na jam'iyyar PDP

Gwamna Douye Diri, yana kokarin neman tazarce kan kujerarsa mai lamba ɗaya a jihar Bayelsa, zango na biyu kuma na karshe kamar yadda kwansutushin ya tanada.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Sanatocin PDP Guda 6 Waɗanda Ka Iya Neman Babban Mukami a Majalisar Dattawa

Babbar matsala da ƙalubalen da zai fuskanta ita ce ɗan takarar APC, Mista Sylva, wanda da yawan masana siyasa ke ganin yana da karfin da zai iya daƙile tazarcen Diri.

A wani labarin kuma Wasu Kungiyoyi Sun Bayyana Shiyyar da Ya Dace Ta Fitar da Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10

Kodinetan gamayyar ƙungiyoyin ya bayyana cewa arewa maso yamma ta baiwa Tinubu ƙari'u mafi yawa har ya samu nasara a babban zaben 2023.

Ya bayyana Sunan Sanata daga jihar Kano a matsayin wanda ya fi cancanta a kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel