Mataimakin Shugaban APC Ya Ba Adamu Wa’adin Kwana 7 Ya Kira Taron NEC

Mataimakin Shugaban APC Ya Ba Adamu Wa’adin Kwana 7 Ya Kira Taron NEC

  • An ba shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu wa'adin sati daya ya kira taron NEC ko ya fuskanci doka
  • Mataimakin shugaban APC na kasa (Arewa maso yamma), Salihu Muhammed Lukman ne ya yi kiran yayin da yake jan hankalin Adamu zuwa ga wasu muhimman batutuwa
  • Lukman, a wata budaddiyar wasika ya bukaci shugaban na APC da ya gudanar da taron don magance muhimman batutuwan jam'iyyar kafin mika mulki ranar 29 ga watan Mayu

Mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki (Arewa maso yamma), Salihu Mohammed Lukman ya tunkari shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu da wani sabon aiki.

An bukaci Adamu da ya kira taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar na kasa wato NEC cikin mako guda ko ya fuskanci doka.

Salihu Lukman da Sanata Abdullahi Adamu
Mataimakin Shugaban APC Ya Ba Adamu Wa’adin Kwana 7 Ya Kira Taron NEC Hoto: Salihu Lukman, Senator Abdullahi Adamu
Asali: Facebook

An ba shugaban APC Adamu sabon aiki gabannin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu

Kara karanta wannan

Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce

A wata budaddiyar wasika zuwa ga Adamu mai kwanan wata 19 ga watan Afrilun 2023, Lukman ya ce ya kamata a kira taron don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi jam'iyyar kafin ranar 29 ga watan Mayu da za a mika mulki, jaridar Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lukman wanda ya kasance mamba na kwamitin aiki na APC na kasa (NWC) ya ce zai dauki mataki na doka kan Adamu idan ya ki amsa bukatarsa, rahoton Punch.

FG ta fadi dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a lamarin Binani da Fintiri a zaben Adamawa ba

A wani labari na daban, Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya magantu kan dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kauracewa hatsaniyar da aka shiga a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An shiga tashin hankali, shugaban APC a wata jiha ya fadi matacce

Mohammed ya ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ce ta san hukuncin da za ayi wa Hudu Yunusa Ari domin wannan ba aikin shugaban kasa ba ne.

Ya jaddada cewar Shugaba Buhari ba ya yi wa hukumomin gwamnati kastalandan, yana barinsu su gudanar da harkokin gabansu yadda ya dace.

Har ila yau, ministan ya nanata cewa gwamnatinsu ta shugaba Muhammadu Buhari da APC ba ta taba yi wa INEC katsalandan a kan ayyukanta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel