Zabe: “Masu Neman a Tsige Shugaban INEC Makiyan Najeriya Ne” - Ogah

Zabe: “Masu Neman a Tsige Shugaban INEC Makiyan Najeriya Ne” - Ogah

  • Kwamrad Chinedu Ogah , dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikwo/Ezza ta kudu a majalisar wakilai ya yaba ma Farfesa Mahmood Yakubu
  • Ogah ya ce makiyan Najeriya ne suke neman a tsige shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
  • A cewar dan majalisa, Farfesa Mahmood ya cancanci yabo a kan gudanarwar zaben 2023

Dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Ikwo/Ezza ta kudu, Kwamrad Chinedu Ogah (OON), ya bayyana cewa wadanda ke kira ga tsige shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, Mahmood Yakubu, makiyan Najeriya ne.

Ogah ya bayyana cewa gaba daya bai dace ba mutane su dunga sukar shugaban hukumar zabe wanda ya yi namijin kokari wajen gudanar da babban zaben 2023, jaridar Vanguard ta rahoto.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Zabe: “Masu Neman a Tsige Shugaban INEC Makiyan Najeriya Ne” - Ogah
Asali: Original

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, Ogah ya kara da cewar wadanda suke ganin ba a yi daidai ba a gudanarwar zaben su nemi gyara a kotu maimakon yi wa shugaban hukumar zaben kaca-kaca.

Kara karanta wannan

Dani za a yi: Tsohon gwamnan jihar Arewa ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa

Shugaban INEC ya yi zabe mafi inganci a kasar, Ogah

A cewarsa, shugaban INEC ya gudanar da daya daga cikin zabuka mafi gaskiya da amana da aka yi a kasar kuma babu wani dalili da zai sa wani ya nemi a tunbuke shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ogah ya ce:

"Shugaban INEC din ya yi kokari sosai. Wadanda ke neman a tsige shi makiyan Najeriya ne. Wasu daga cikin mutanen nan basu ma yi zabe ba a lokacin zaben amma yanzu suna buga wasa da lamarin saboda son zuciyarsu.
"Mun yaba da sakamakon zaben. Mun taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a zaben. Zabensu nufi ne na Allah. Ya rage ga bangaren shari'a su taka nasu rawar ganin."

Dan majalisar ya kuma jaddada cewa akwai bukatar yan Najeriya su dunga yaba ma kokarin jami'an gwamnati da suka yi kokari a aikinsu, maimakon yin zargi mara tushe a kansu, rahoton Opera News.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

PDP ta dakatar da shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) ta sanar da dakatar da shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris.

Kwamitin gudanarwa na PDP a gudunmar Igyorov da ke karamar hukumar Gboko ta jihar Benue ce ta dakatar da Ayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel