‘Arewa Maso Yamma Ce Ta Ba Tinubu Kuri’u Mafi Yawa’: Yari Ya Shiga Jerin Masu Neman Kujerar Shugaban Majalisa

‘Arewa Maso Yamma Ce Ta Ba Tinubu Kuri’u Mafi Yawa’: Yari Ya Shiga Jerin Masu Neman Kujerar Shugaban Majalisa

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa ta Najeriya
  • Abdulaziz Yari ya bayyana hujjojinsa da yadda yake jin shi ne ya fi cancanta ya maye gurbin Ahmad Lawal nan kusa
  • An yi zabe a Najeriya, ‘yan siyasa daga bangarori da yawa na nuna sha’awarsu ga kujerar majalisar dattawa ta kasa

Jihar Zamfara - Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban majalisar dattawa ta Najeriya.

Yari ya bayyana hakan ne tare da bayyana hujjar cewa, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi ba dan takarar shugaban kasa na APC kuri’u mafi a zaben shugaban kasa na bana.

Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu, inda ya samu jumillar kuri’u 2,652,235 daga Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Tsohon gwamnan Zamfara ya shiga sahun masu neman maye gurbin Ahmad Lawal
Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yari dai sanata ne da zai wakilci Zamfara ta Yamma a majalisar dattawa ta 10 na tsawon shekaru hudu kafin a sake zabe a 2027.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hujjojin da Yari ya bayyana

A wani bidiyon da Imran Muhammad ya yada a Twitter, an ji jigon na APC kuma tsohon gwamnan Zamfara na cewa:

“Zabe ya zo, ya tafi kuma dai shiyyar (Arewa maso Yamma) ta yi abin da ake zato na jan ragamar kawo kuri’u ga zababben shugaban kasarnmu da jam’iyyarmu.
“Duk da dai wasu mutane sun so kawo tsaiko ga hakan, amma mun yi iyakar kokari duk kuwa da kalubalen da aka samu.
“Yanzu, muna da shugaban kasa (Tinubu) daga Kudu maso Yamma, muna da mataimakin shugaban kasa daga Arewa maso Gabas sannan Arewa maso Yamma na jira.
“Na yi imanin cewa idan shiyyata za ta yanke shawarin goyon bayana ba za ta goyi bayan wanda bai dace ba. Na yi imanin sun san kokari na tun daga matakin shugaban jam’iyya, dan majalisa har zuwa gwamna.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

Yari dai zai gwabza ne da jiga-jigan ‘yan siyasa a Najeriya da ke neman wannan kujera ta shugaban majalisa irinsu Jibrin Barau, David Umahi, Orji Kalu, Ali Ndume da Godswill Akpabio.

Yari da badakalar kudade

A watan Mayun 2022, hukumar EFCC ta zargi Yari da kalmashe wasu kudaden da ke alaka da shirin tallafi na SURE-P.

An kuma kama tsohon gwamnan na Zamfara bisa zarginsa da hannu a badakalar Ahmed Idris, korarren akanta-janar na Najeriya.

An sha kai ruwa rana da ‘yan siyasan Najeriya kan badakalar kudade da kuma sace kadarar kasa tare da zuba wa a lalitarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel