Daga Dakatar da Shi, Tsohon Gwamnan Katsina Yana Barazanar Barin PDP Nan da Awa 48

Daga Dakatar da Shi, Tsohon Gwamnan Katsina Yana Barazanar Barin PDP Nan da Awa 48

  • Idan ba a dauki mataki ba, zaman Ibrahim Shehu Shema a Jam’iyyar PDP ya zo karshe
  • Tsohon Gwamnan Katsina ya rubuta wasika zuwa ga NWC a kan dakatar da shi da aka yi
  • Ibrahim Shehu Shema ya nuna ba zai yarda da canza shugabannin PDP na jihar Katsina ba

Katsina - Ibrahim Shehu Shema wanda ya yi Gwamna a jihar Katsina, ya bukaci shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, ya janye dakatarwar da ya yi masa.

Barista Ibrahim Shehu Shema ya ce muddin Sanata Iyorchia Ayu bai janye wannan mataki ba, kuma bai dawo da shugabannin PDP a Katsina ba, zai sauya-sheka.

Premium Times ta ce tsohon Gwamnan ya yi wannan barazana ne a wata wasika da ya aikawa uwar jam’iyya, kuma har ya shiga hannunta a ranar Juma’ar nan.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa PDP Raddi Mai Ban Tsoro Bayan Dakatar da Shi Daga Jam’iyya

‘Dan siyasar ya bukaci a gaggauta dawo da shugabannin PDP na reshen Katsina da aka dakatar, ya ce uwar jam’iyya ta saba doka wajen ruguza shugabannin jihar.

Dakatar da su daga Jam'iyya

Wasikar ta zama martani a kan dakatar da shi da aka yi tare da wasu jagororin PDP a jiya, NWC ta kafa hujja da sassa na 29(2)(b) da na 31(2) E na dokar jam’iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wasikar da ya aika zuwa Hedikwatar PDP a Abuja, Shema ya ce sanarwar da NWC ta bada ta yawun Debo Ologunagba ya ci karo da abin da dokar PDP ta ce.

Shema
Wasikar Ibrahim Shema Hoto: @SirTogish
Asali: Facebook

An sabawa doka - Barista Shema

A matsayinsa na ‘dan majalisar koli ta NEC kuma daya daga cikin ‘yan majalisar amintattu na BOT, baya ga kasancewarsa ‘dan cikin gida, Shema ya soki PDP.

Kara karanta wannan

APC ta Dakatar da SGF, Jam’iyya na Binciken Sanata, An Jero Zargin da Ake Yi Masu

Baristan ya ce akwai matakan da ake bi kafin dakatar da mutum, tsohon Gwamnan na Katsina ya ce NWC tayi wa sashe na 56 (6) (7) da 59 (3) hawan kawara.

An rahoto Shema wanda ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyya na reshen Arewa maso yamma kafin 2007 yana kokawa a kan taba majalisar SWC.

Takardar ‘dan siyasar ta ba Ayu da ‘yan majalisarsa sa’o’i 48 da su lashe amansu, su dawo da shugabannin PDP na reshen Katsina ko kuwa ya bar jam’iyyar.

Legit.ng Hausa ta fahimci muddin uwar jam’iyya ba tayi abin da ‘dan siyasar ya kenema ba, nan da zuwa karshen makon za a iya jin sanarwa mara dadi.

Fayose ya tanka NWC

Ayodele Fayose yana cikin jerin ‘Yan siyasar da PDP ta dakatar da su a Najeriya, kuma an ji labari ya ce nan da ‘yan kwanaki za ayi waje da Iyorchia Ayu.

Hakan yana nufin jam’iyyar za ta iya tsumbulawa cikin wani sabon rikicin shugabanci. Tsohon Gwamnan na Ekiti ya ce dakatar da shi ba za tayi aiki ba.

Kara karanta wannan

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

Asali: Legit.ng

Online view pixel