Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

  • Atiku Abubakar ya ce ba tsakani da Allah ya rasa zaben 2023, magudi Hukumar INEC ta shirya
  • ‘Dan takarar kujerar shugaban kasan ya ce zai kira masu shaida domin tabbatar da gaskiyarsa
  • Lauyan ‘dan takaran, Joe-Kyari Gadzama SAN ya fadawa kotun zabe yadda aka shirya magudi

Abuja - Atiku Abubakar da ya nemi kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya zargi hukumar INEC da dauke masa kuri’u a zabe.

Wani labari da aka fitar a Premium Times, ya rahoto Atiku Abubakar yana mai cewa an kwashe kuri’un da aka kada masa, aka ba APC nasara.

A korafin da ‘dan takaran ya rubutawa kotun sauararon karar zabe da ke zama a Abuja, ya ce da gangan hukumar INEC ta yi masa coge a zabe.

Lauyoyin Atiku a karkashin jagorancin Joe-Kyari Gadzama SAN, sun yi karar INEC, Tinubu da APC, su na masu yin alwashin ba PDP nasara.

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

An taba BVAS da IRev?

Joe-Kyari Gadzama yake cewa na’uraron BVAS da aka shirya domin aika sakamakon zabe kai tsaye ba su yi aikin da ya kamata a zaben ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan da ya tsayawa ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP mai adawa ya ce jami’an INEC sun yi wasa da hankalin shafinsu na IRev.

Atiku
Atiku a wajen zabe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Kyari Gadzama SAN ya jefi INEC da zargin sai sun tace sakamako kafin su daura shi a shafin, hakan ya jawo aka ce Bola Tinubu ya ci zabe.

Rahoton ya ce Lauyoyin da aka dauka sun fadawa kotun karar zaben shugaban kasa cewa Hukumar zabe ba ta yi amfani da doka da sharudan aikinta ba.

Har ila yau, Atiku Abubakar yana ganin an yi watsi da abin da kundin tsarin mulki ya ce. Jaridar Vanguard ta kawo wannan rahoto a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

"Karya aka yi da sunan na'ura"

A cewar ‘dan takaran, na’urori ba su samu wata matsala kamar yadda ake ikirari ba, ya ce da gan-gan aka ki aika sakamakon zabe domin ayi magudi.

Domin tabbatar da gaskiyarsa a kotu, Atiku zai kira kamfanin kasar Afrika ta Kudu, Kaspersky Endpoint Security zuwa kotu domin su bada shaida.

Haka zalika kamfanin Globacom Nigeria da aka yi amfani da su wajen sadarwa za su yi magana a kotu.

Yaki a APC

A Adamawa, an ji labari Shugabannin APC sun dakatar da Boss Mustapha, sun ce bai yi amfanin komai a zaben shugaban kasa da na Gwamnoni ba.

Sannan jam’iyyar APC ta kafa kwamiti na binciken Sanatan Gombe ta tsakiya a kan zargin zagon kasa, za a gama binciken nan da makonni biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel