Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

  • Tun farko Atiku Abubakar yana ganin Bola Tinubu bai halatta ya tsaya neman mulkin Najeriya ba
  • ‘Dan takaran na Jam’iyyar PDP ya ce Hukumar INEC tayi kuskure da ta ba APC nasara a zaben 2023
  • Lauyoyin Atiku da na Peter Obi duk sun shiga kotu, kowa yana ikirarin shi zai zama shugaban kasa

Abuja - Atiku Abubakar wanda ya tsayawa jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, ya shigar da kara a kotu, yana kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

Vanguard ta ce Alhaji Atiku Abubakar yana ikirarin ayyana Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ba daidai ba ne.

A karar da ya shigar mai lamba CA/PEPC/05/2023 a kotun sauraron karar zabe, ‘dan takaran PDP ya bukaci INEC ta karbe nasarar da ta ba Tinubu.

Kara karanta wannan

Jerin Abubuwa 5 Da Obi Ya Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Masa A Yayin Da Ya Ke Kallubalantar Nasarar Tinubu

Wazirin Adamawa yake cewa ba a bi dokar zabe ta 2022 ba, don haka sanar da ‘dan takaran APC a matsayin wanda ya yi galaba, kuskure ne a doka.

Tinubu bai ci zabe ba

Babban Lauya Joe Kyari Gadzama SAN ya ce Tinubu ya samu nasara ne ta haramtacciyar hanya, kuma bai da rinjayen kuri’un da aka kada.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga haka, rahoton ya ce Joe Gadzama SAN yana ikirarin tun farko bai dace tsohon Gwamnan na Legas ya shiga takarar shugaban Najeriya ba.

Atiku
Atiku a wajen kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: UGC

Abin da Atiku Abubakar yake so shi ne a ruguza nasarar jam’iyyar APC, sannan a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe kuma yake jiran gado.

‘Dan siyasar yake cewa shi ya kamata a ba nasara domin ya zo na biyu da kuri’u kusan miliyan bakwai a zaben da aka yi a karshen watan Fubrairu.

Kara karanta wannan

Ba Za Ku Iya Kwace Wa Tinubu Nasarsa Ba, APC Ta Yi Martani Ga Obi

PDP da LP su na kotu

A daren Laraba Lauyoyin Atiku Abubakar suka shigar da wannan kara a kotun da ke Abuja.

A daidai wannan lokacin ne shi ma Peter Obi ya shigar da kararsa yana mai rokon a soke nasarar da hukumar INEC ta ba ‘dan takaran jam’iyyar APC.

Obi wanda ya yi takara a LP ya ce a doka, Tinubu bai da damar tsayawa takara domin kotun Amurka ta taba samun shi da laifi, aka ci sa tarar $400, 000.

Zargin magudin zabe

An ji labari Rotimi wanda ya yi Gwamna a jihar Ribas, ya ce Shugaban INEC yana da alaka da Bola Tinubu da kuma Gwamna Nyesom Wike.

Amaechi yana cewa 'Yan sanda su na taimakawa PDP wajen cafke ‘yan APC da SDP, tsohon Ministan ya zargi hukuma da hannu a magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel