Gwamnan Nasarawa: Jam’iyyun Siyasa 4 Sun Yi Maja Don Tsige Gwamna Sule

Gwamnan Nasarawa: Jam’iyyun Siyasa 4 Sun Yi Maja Don Tsige Gwamna Sule

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, zai sha gwagwarmaya a kokarin da yake yi na son zarcewa kan kujerarsa
  • Manyan jam'iyyun siyasa 4 na shirin yin maja don lallasa gwamnan na APC a zaben ranar Asabar, 18 ga watan Maris a jihar
  • Jam'iyyun siyasar 4 da ke shirin aiki tare sun hada da NNPP, SDP, AA da PRP kuma yan takararsu sun yi watsi da rahoton cewa sun janyewa gwamnan

Nasarawa - Kudirin Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa na son zarcewa na fuskantar barazana yayin da jam'iyyun siyasa 4 ke shirin yin maja gabannin zaben gwamnoni.

Jam'iyyun na shirin hadewa ne a kokarinsu na tsige dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Jaridar Daily Independent ta rahoto cewa jam'iyyun siyasar 4 da suka yi maja sune Social Democratic Party (SDP), Peoples Redemption Party (PRP), New Nigeria People’s Party (NNPP), da Action Alliance (AA).

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Jam'iyyu 5 Sun Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Gwamna Abdullahi Sule yana jawabi
Gwamnan Nasarawa: Jam’iyyun Siyasa 4 Sun Yi Maja Don Tsige Gwamna Sule Hoto: The Cable
Asali: UGC

Jerin jam'iyyun da ke shirin maja don fatattakar APC

Yan takarar gwamnan jam'iyyun, Mustapha Abubakar (SDP), Sen. Yusuf Musa Nagogo (PRP), Abdullahi Yakubu Maidoya (NNPP) da Alaku Godwin (AA), duk sun yarda su rushe tsarinsu zuwa daya don lallasa gwamna Sule mai ci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maidoya ne ya bayyana shawarar da yan takarar suka yanke a wani taron manema labarai a Lafia, babban birnin jihar a madadin yan takarar hudu a ranar Talata, 14 ga watan Maris.

Sun kuma yi watsi da rahoton cewa yan takarar za su ruguza tsarinsu ne ga Gwamna Sule na APC a zabe mai zuwa a jihar.

Maidoya ya jaddada cewa nan ba da jimawa ba jam'iyyun hudu za su yi maja don aiki tare a zaben gwamnan da za a yi nan da kwanaki 4.

Kara karanta wannan

2023: Kwana 4 Gabanin Zabe, 'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye Daga Takara

Dan takarar na NNPP ya ce za a sanar da jama'a da magoya bayansu a jihar batun majan.

Zaben Gwamna: Kungiyar CAN ta aike ga muhimmin sako ha Kiristocin Neja

A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Neja ta yi kira ga mabiya addinin Kiristanci da su dubi cancanta yayin zaben wanda zai jagorance su a zaben ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel