Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Ambaci Matsala 1 da Za a Iya Fuskanta a Gobe

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Ambaci Matsala 1 da Za a Iya Fuskanta a Gobe

  • Farfesa Attahiru Jega ya ce za a iya yi wa INEC kutse tun da yanzu bayananta su na kan yanar gizo
  • Tsohon shugaban hukumar ta INEC ya ce a zamanin da ake ciki yau, ba a rasa ja’irai masu yin kutse
  • Jega yana ganin ba a canza Nairori a lokacin da ya dace ba, domin an bukatar kudi lokacin yin zabe

Abuja - Tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce yin kutse cikin harkar zaben Najeriya yana iya yiwuwa.

A wata zantawa da aka yi da shi a tashar talabijin Trust TV, Farfesa Attahiru Jega ya nuna yiwuwar masu kutse su aukawa uwar garken hukumar.

An tattauna da tsohon shugaban na INEC ne a kan shirin da aka yi domin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar wakilan tarayya da dattawa.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso Za Su Raba Kuri’u Miliyan 87 Nan da Awa 24

A zaben nan na 2023, Hukumar INEC ta fito da na’uar BVAS da za a rika amfani da ita wajen tantance mutum kafin ya samu damar kada kuri’arsa.

An kawo na'urar BVAS

Daily Trust ta ce da BVAS ake amfani wajen duba katin PVC, sannan sai a aika da bayanan masu yin zabe zuwa wata matattara da INEC tayi tanadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Attahiru Jega ya yabi irin shirin da jami’an zabe suka yi domin gobe, amma ya ce hakan bai bada tabbacin ba za a iya yi wa matattarar kutse ba.

INEC.
Ana shirin zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Farfesan ya ce a irin wannan zamani, ana iya yin kutse muddin aka daura abu a kan yanar gizo.

“Ka ga a wannan zamanin na cigaba, babu wanda zai iya ba ka tabbas 100% ba za a iya yi wa matattar bayanan kutse ba, sai dai idan bai kan yanar gizo

Kara karanta wannan

Ganin an Canza Nairori, ‘Yan Siyasa Sun Fito da Sabon Dabarar Yin Magudi Inji EFCC

A shekarar 2015 mun yi zaben, matattarar bayananmu ba ta kan yanar gizo. Yanzu saboda akwai batun aika sakamako ta na’ura, dole ya shiga yanar gizo.
Amma ko ina a fadin Duniya ana amfani da uwar garke, kuma akwai kariya babu laifi domin mutane su na tanadar na’urorin hana yin kutse.”

- Farfesa Attahiru Jega

Rahoton ya ce malamin jami’ar ya tabbatar da cewa INEC sun yi kokari wajen bada tsaro. A game da batun canza kudi kuwa, yana ganin an yi kuskure.

Lissafin zaben 2023

A wani rahotonmu, kun ji duk da Bola Tinubu yana tare da Gwamnoni 21 da Sanatoci kusan 65, canjin kudi da bakin jinin APC zai iya kawo masa cikas.

Sannan Duk da karfin PDP da kwarewar Atiku Abubakar, tsohon abokin takararsa watau Peter Obi zai bata masa lissafi musamman a jihohin Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel