PDP: Wani Tsohon Minista Suka Canza Kudi da Tinubu Ya Doke Shi, Zai Ci Amanar APC

PDP: Wani Tsohon Minista Suka Canza Kudi da Tinubu Ya Doke Shi, Zai Ci Amanar APC

  • Kwamitin yakin neman zaben PDP ya ce Rotimi Chibuike Amaechi yana tare da Atiku Abubakar
  • Darektan kwamitin na PDPPCC ya zargi Amaechi da hannu wajen kawo tsarin canza takardun kudi
  • Jam’iyyar APC tayi wa Ogbonna Nwuke raddi, ta na mai nesanta tsohon Ministan daga wannan zargi

Rivers - Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar Ribas, ya jero Rotimi Chibuike Amaechi a cikin masu hannu wajen canza takardun kudi.

Punch ta ce kwamitin PDPPCC ya ce da hannun tsohon Gwamnan Ribas a wahalar fetur da ake fama da shi da kuma tsarin sauya kudi da takaita yawonsu.

Darektan yada labarai da sadarwa na kwamitin yakin takarar PDP, Ogbonna Nwuke ya kalubalanci Rotimi Amaechi ya musanya zargin jefa al’umma a kunci.

Baya ga haka, The Nation ta rahoto kwamitin ya ce tsohon Ministan sufurin yana yi wa PDP aiki.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Makarantan Legit.ng Sun Tsaida ‘Dan Takara Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP

Amaechi ya yi sulhu da 'Yan PDP

A cewar Cif Ogbonna Nwuke, Amaechi ya sasanta da ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar PDP na reshen Ribas, har ya yi zama a boye da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Darektan na PDPPCC a jihar Ribas ya ce ya yi wasu zama a asirce tare da ‘dan takaran PDP watau Alhaji Atiku Abubakar, kuma shi yake marawa baya a 2023.

'Yan PDP
Atiku Abubakar a taron siyasa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

"An wahalar da ‘Yan Najeriya su na neman kudin da za su yi cefane, su ciyar da iyalinsu.
Abin da mafi yawan mutanen Najeriya ba sus ani ba shi ne, miyagun da suka jawo wannan wahala sun yi da gan-gan ne saboda ya yi tasiri a zabe mai zuwa."

- Ogbonna Nwuke

Jam'iyyar APC ta maida martani

The Cable ce reshen jam’iyyar APC da ke tare da Amaechi a jihar Ribas ta yi wa Nwuke raddi, tana cewa a rude yake, kuma bai san abin da yake fada ba.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

Sakataren yada labaran APC, Darlington Nwauju ya tunawa Darektan kamfen din yadda Nyesom Wike ya ce yanzu tsohon Ministan bai iya shiga Aso Villa.

Bayan an gama cewa an yi fatali da Amaechi daga fadar shugaban kasa, sai ga shi ‘yan PDP su na ikirarin yana cikin miyagu da ke rike da akalar gwamnati.

A ra’ayin Ogbonna Nwuke, ana kokarin hada kai da ‘Dan Amanar Daura wajen ganin an murkushe mutanen Kudancin Najeriya, a hana su zabinsu a zaben bana.

Atiku zai ci zabe - 'Diyarsa

A wani rahoto da muka fitar dazu, an ji Hauwa Atiku-Uwais ta fadi dalilin mahaifinsu na yawan neman takara da kuma amfanin irin manufofinsa.

Hauwa Atiku-Uwais ta ce idan aka bada dama ‘yan kasuwa suka shigo Najeriya, za a samu kamfanoni da su ke yin aiki, hakan zai jawo karin haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel