Shugaban Kasa: Makarantan Legit.ng Sun Tsaida ‘Dan Takara Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP

Shugaban Kasa: Makarantan Legit.ng Sun Tsaida ‘Dan Takara Tsakanin APC, PDP, NNPP da LP

  • Mun tambayi masu karanta labaranmu game da wanda suke so ya zama Shugaban kasar Najeriya
  • Mafi yawan wadanda suka shiga zabenmu sun nuna ba su tare da manyan jam’iyyun APC da PDP
  • ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya fi Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Bola Tinubu farin jini a zaben na mu

Abuja - Ganin zaben shugaban kasa ya zo, Legit.ng Hausa ta bude filin jin ra'ayi na musamman domin sanin inda makarantamu suka sa a gaba.

Mun tambayi masu bibiyar shafinmu a Twitter cewa a cikin manyan 'yan takaran shugabancin kasar nan, wane za su zaba a mako mai zuwa.

Mutane 5, 596 suka kada kuri’arsu a wannan zabe da aka shirya wanda aka yi kusan kwana biyu ana fafatawa, a karshe Peter Obi ne ya yi galaba.

LP ta doke APC, PDP da NNPP

‘Dan takaran jam’iyya mai mulki ta APC watau Asiwaju Bola Tinubu ya zo na hudu a zabenmu, ya samu kuri’u 588 ne da ke wakiltar kashi 10.5%.

Wanda ya zo na uku a zaben shi ne Atiku Abubakar mai neman takara a PDP. Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya samu kuri’un mutane 856.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Na biyu a zaben da jama’a suka yi shi ne Rabiu Kwankwaso wanda ya tsaya a jam’iyyar NNPP, yana da mutane 1533 watau 27.4% na kuri’un.

Shugaban Kasa
Peter Obi a Owerri Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Peter Obi mai neman mulki a jam’iyyar LP ya fi kowa kaso mai tsoka a filin zaben da mu ka shirya, mutum 2613 da ke wakiltar 46.7% shi suka zaba.

Ga yadda sakamakon zaben yake a kasa:

  1. Asiwaju Bola Tinubu (APC) - 10.5%
  2. Atiku Abubakar (PDP) - 15.3%
  3. Peter Obi (LP) - 46.7%
  4. Rabi'u Kwankwaso (NNPP) - 27.4%

Amma mafi yawan masu magana musamman daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna cewa Rabiu Kwankwaso za su ba kuri’arsu a zaben bana.

Wasu kuma sun nuna cewa Atiku Abubakar shi ne mafita a takarar shugabancin kasar nan.

NNPP tayi babban rashi

A daren yau aka tabbatar da labarin rasuwar Hon. Kamilu Ado Wudil wanda yake takarar 'dan majalisa a mazabar Garko da Wudil a zaben 2023.

‘Dan takaran NNPP a zaben ‘dan majalisar wakilan tarayyar Wudil/Garko ya rasu ne ana kusan saura mako daya ayi zaben da yake hangen nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel