PDP Ta Yi Babban Rashi a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja a NNPP

PDP Ta Yi Babban Rashi a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja a NNPP

  • Yan kwanaki kafin babban zaben 2023, jam'iyyar PDP ta gamu da gagarumin cikas a jihar Kano
  • PDP tsagin da Shehu Sagagi ke jagoranta a Kano sun rushe tsarinsu a cikin jam'iyyar NNPP ta su Rabiu Musa Kwankwaso
  • Sagagi sun yasar da Atiku Abubakar sun zabi Kwankwaso a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa

Kano - Tsagin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Shehu Sagagi ke jagoranta a jihar Kano sun yi maja a cikin jam'iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP.

Wannan ci gaban na zuwa ne kimanin shekara daya bayan sun sauya sheka daga jam'iyyar, jaridar PM News ta rahoto.

Rabiu Kwankwaso
PDP Ta Yi Babban Rashi a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja a NNPP Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Masu sauya shekar sun bayyana dalilinsu na ficewa daga jam'iyyar

Sagagi ya ce ya bar PDP ne saboda rashin damokradiyyar cikin gida da son zuciya na shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tinubu Zai Shayar Da Atiku Mamaki a Arewa Maso Gabas - APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har wayau, ya ce ya fice ne don amanna da ya yi cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan FGabrairu.

Ya kuma yi ikirarin cewa ya sauya sheka zuwa NNPP tare da shugabannin jihar 36, fiye da shugabanni 700 na kananan hukumomi, shugabannin guduma su 8,000, deleget din PDP na kasa 44 da deleget na gudunma su 1,452.

Sanusi Dawakin Tofa, kakakin kwamitin yakin neman zaben NNPP, ya nakalto Sagagi yana cewa:

"Siyasa magana ce ta yawa, muna da yakinin cewa dan takarar shugaban kasa na NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kai mu ga nasara a matakin kasa da na jiha.
"Jam'iyyar PDP ta yi wa kanta zagon kasa a jiha kamar Kano ta hanyar bari mutum kamar Sanata Kwankwaso ya sauya sheka duk da tarin mabiya da yake da su a fadin kasar ba ma a iya jihar ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Kira Zaman Gaggawa Da Gwamnoninta Gobe Lahadi

"A garemu tamkar gida muka koma, mu ne ainahin yan siyasa kuma mun hade da jam'iyyar siyasa da ke buga ainayin siyasa.
"Ina farin cikin sake hadewa da Sanata Kwankwaso shekara daya bayan rabuwarmu," "

Masu sauya shekar sun samu tarba cikin NNPP daga shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Rufa'i Alkali da abokin takarar Kwankwaso, Isaac Idahosa, a wani taro da aka gudanar a Kano.

Alkali ya taya masu sauya shekar murnar wannan zabi na hikima da suka yi na dawowa NNPP.

A nashi bangaren, Idahosa ya bayyana cewa da wannan gagarumin goyon baya da NNPP ke samu da kuma sauya sheka mai dumbin tarihi za su yi nasara a zaben, rahoton Vanguard.

Na yi mamaki da jin gwamnonin APC suna zagin Buhari

A wani labarin, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya cika da mamaki da jin cewa wasu gwamnoni na zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan manufar sauya kudi.

Kwankwaso ya ce wannan manufar sauya kudin y.a yi amfani sosai domin dai wadanda suka tara biliyoyin kudi a gidajensu ya zama basu da amfani

Asali: Legit.ng

Online view pixel