Yanzu Yanzu: Magoya Bayan Tinubu Da Ribadu Sun Sauya Shaka Zuwa PDP a Jihar Adamawa

Yanzu Yanzu: Magoya Bayan Tinubu Da Ribadu Sun Sauya Shaka Zuwa PDP a Jihar Adamawa

  • Jam’iyyar APC ta rasa mambobin kungiyoyin goyon bayanta biyu a jihar Adamawa inda suka koma PDP gabannin zaben 2023
  • Mambobin kungiyar goyon bayan Nuhu Ribadu da na Gidauniyar Tinubu sun fice daga APC kwanaki shida kafin zabe
  • Jagoran kungiyar Tinubu Foundation a jihar, Suleiman Yarima, ya bayyana dalilin da yasa suka koma PDP

Jihar Adamawa – Kwanaki shida kafin zaben shugaban kasa na 2023, mambobin kungiyar goyon bayan Nuhu Ribadu da na Gidauniyar Tinubu a jihar Adamawa sun sauya sheka zuwa PDP.

Jagoran kungiyar Tinubu Foundation a jihar, Suleiman Yarima, ne ya sanar da sauya shekarsu a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu.

Okowa da Atiku
Yanzu Yanzu: Magoya Bayan Tinubu Da Ribadu Sun Sauya Shaka Zuwa PDP a Jihar Adamawa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Yarima ya jagoranci daruruwan mambobin kungiyoyin zuwa wajen Gwamna Umaru Fintiri a gidan gwamnati da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku Yaba Tinubu Ƙafa a Arewa, Ɗaruruwan Ƴan APC Sun Koma PDP Gabanin Zaɓe

Dalilin da yasa muka fice daga APC, Suleiman

Yarima ya ce kungiyoyin sun sauya sheka zuwa PDP ne saboda gagarumin nasarar da aka samu a gwamnatin Fintiri a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wasu daga cikin mambobin kungiyar na cikin wadanda suka samar da jerin sunayen yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar kuma sun sha alwashin cewa magoya bayan za su zabi PDP a zabe mai zuwa.

Za mu tabbatar da zarcewar Fintiri – Aliyu

Hakazalika da yake magana, shugaban kungiyar goyon bayan Ribadu, Alh Saidu Aliyu, ya ce za su tabbatar da tazarcen Fintiri da sauran yan takarar PDP a jihar.

A martaninsa, gwamnan ya yi godiya ga kungiyoyin kan ayyana goyon bayansu ga PDP sannan ya yi alkawarin aiki da su.

Yan Najeriya sun yi martani

Ukpai Emma Ukpai ya yi martani a Facebook:

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

“Ina taya ka murna ya mai girma Atiku Abubakar."

Abubakar Ibrahim Waziri ya ce:

“Akwai karin wasu masu zuwa.”

Said Hamid ya ce:

“Yanzu abubuwa na tafiya daidai sai Atiku Insha Allah."

Ba zan koma APC ba - Gwamna Nyesom Wike

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nywsom Wike ya sake yin watsi da rade-radinm cewa zai koma jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Wike jaddada cewar yana nan daram-dam a jam'iyyar PDP amma ya yi sha'awar tsarin APC na karba-karba don hadin kan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel