APC Ta Samu Koma Baya Ɗaruruwan Magoya Bayanta Sun Koma PDP

APC Ta Samu Koma Baya Ɗaruruwan Magoya Bayanta Sun Koma PDP

  • Tafiyar neman ƙwato mulki a hannun PDP da APC ke yi a jihar Adamawa ta samu koma baya
  • Wasu ɗaruruwan magoyan bayan Tinubu da Ribadu a jihar sun fice daga jam'iyyar APC sun koma PDP
  • Mambobin sun tabbatar da cewa za su yi dukkanin mai yiwuwa domin ganin PDP tayi nasara a zaɓen dake tafe

Mambobin wata ƙungiya mai goyon bayan Tinubu da Nuhu Ribadu a jihar Adamawa sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a jihar.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana biyar kafin babban zaɓen 2023. Rahoton Daily Trust.

PDP da APC
APC Ta Samu Koma Baya Ɗaruruwan Magoya Bayanta Sun Koma PDP
Asali: Twitter

Jagoran ƙungiyar, Suleiman Yarima, shine ya sanar da ficewar su daga tafiyar APC a gidan gwamnatin jihar a Yola, babban birnin jihar Adamawa a ranar Litinin, lokacin da ya jagoranci ɗaruruwan mambobin ƙungiyar zuwa gaban gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Ya Shiga Takarar Gwamna

Suleiman ya bayyana cewa komawar su PDP ya zama tilas duba da irin nasarorin da gwamnatin Fintiri ta samu a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace wasu daga cikin mambobin suna cikin ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na jihar sannan sun sha alwashin cewa PDP za su kaɗa wa ƙuri'un su.

Magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Adamawa sun sha sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP, Rahoton Guardian.

Haka kuma, Alhaji Saidu Aliyu, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar, yace za su tabbatar cewa Fintiri ya sake ɗarewa kan kujerar sa sannan an zaɓi dukkanin ƴan takarar PDP daga sama har ƙasa.

Gwamnan ya nuna godiyar sa kan yadda suka nuna goyon bayan su ga jam'iyyat PDP, sannan ya kuma yi musu alƙawarin zai dama dasu a gwamnatin sa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Kutsa Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10, Bayanai Sun Fito

Jam'iyyar ADC Ta Janye Daga Neman Shugaban Kasa, Ta Koma Bayan Peter Obi

A wani labarin na daban kuma wata jam'iyya ta haƙura da takarar shugaban ƙasa a zaɓen dake tafe, ta amince ta marawa ɗan takarar jam'iyyar adawa baya.

Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi gabanin zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Jam'iyyar ADC ta sanar da wannan matakin na ta na komawa bayan takarar Peter Obi a yayin wani taron yan jarida a birnin tarayya Abuja ranar Litinin,

Asali: Legit.ng

Online view pixel