Zaben 2023: Ba Zan Koma APC Ba, Inji Gwamna Nyesom Wike

Zaben 2023: Ba Zan Koma APC Ba, Inji Gwamna Nyesom Wike

  • Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya sake watsi da rade-radin cewa zai koma APC
  • Wike ya ce shi da PDP mutu ka raba amma tsarin karba-karba na APC ya matukar burge shi don sun nuna dattako
  • Saura kwanaki biyar a yi babban zaben shugaban kasa inda za a zabi magajin Buhari tsakanin Atiku na PDP, Tinubu na APC, Obi na LP da Kwankwaso na NNPP

Rivers - Gwanmnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake yin watsi da rade-radin cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), rahoton Vanguard.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar sarakunan gargajiya na jihar Ribas karo na 114 wanda ya gudana a Port Harcourt a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

Nyesom Wike
Zaben 2023: Ba Zan Koma APC Ba, Inji Gwamna Nyesom Wike Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

APC ta buirge ni da tsarin karba-karba, Wike

Gwamnan ya ce har gobe shi dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne duk da cewar tsarin APC na karba-karba ya burge shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Punch ta nakalto Wike yana cewa:

"Ni ba dan APC bane kuma ba zan taba zama ba. Amma, sun sa na gane cewa su jaruman kasar nan ne. Gwamnonin APC sun fito da batun hadin kan kasar nan, cewa ya kamata shugabanci ya koma yankin kudu.
"Sun ce suna son hadin kan kasar nan kuma daboda haka, dole shugabanci ya koma yankin kudu. Da suna iya cewa a'a, amma hakan ba wani abu bane. A matsayin gwamnoni muna da yawan. Har wayau muna iya cewa ya tsaya a inda ya kamata ya tsaya. Amma ba su yi haka ba.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

"Suka ce yadda muke ganin kasar nan muna so kowa ya kasancewa tsintsiya daya. Kada wani ya ce saboda ina da da yawan mutane, don haka, za ka ci gaba da mamaya. A mulki kana bukatar zaman lkafiya, idan ba zaman lafiya ba za ka iya shugabanci ba.
"Mu yan Najeriya ne kuma muna son hadin kan kasar nan, muna son Najeriya ta ci gaba a matsayin kasa mai hadin kai. Ribas ta dade tana goyon bayan Najeriya daya kuma za mu ci gaba da goyon bayan Najeriya daya. Amma wajen yin haka, mun yarda da daidaito, gaskiya da adalci. A matsayin gwamnan jihar, zan zabi hadin kan kasar nan. Zan zabi duk wani abu da zai kawo hadin kan Najeriya."

PSC ta cire sunan Naja'atu cikin masu aikin zabe

A wani labarin, hukumar PSC mai kula da ayyukan yan sanda ta janye sunan tsohuwar jigon APC, Na'ja'atu Muhammad daga cikin jagororin da za su kula da ayyukan jam'ian yan sanda da ke bakin aiki a lokacin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel