‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Hasashen Yadda Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance a Kano

‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Hasashen Yadda Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance a Kano

  • Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce babu wanda ya isa ya gaji kuri’un Muhammadu Buhari a Kano
  • Wannan ya sa aka ji Salihu Tanko Yakasai yana cewa hakan ya yi daidai da hasashen da shi ya yi
  • ‘Dan takaran na Jam’iyyar PRP ya ba NNPP nasara a kan PDP da APC zaben Shugaban kasa

Abuja - Yusuf Datti Baba-Ahmed yana ganin cewa zaben 2023 zai sha bam-bam da sauran zabukan da aka rika yi a baya a tarihin Najeriya.

An rahoto Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce a zabe mai zuwa, babu jam’iyyar da za ta iya gaje kuri’un Muhammadu Buhari a jihar Kano.

A zaben 2015, sai da Muhammadu Buhari ya samu kuri’a kusan miliyan biyu a takarar shugaban kasa da ya tsaya da Goodluck Jonathan.

A yanzu Shugaba Buhari yana shirin kammala wa’adinsa, don haka ba zai tsaya takara ba, Datti Baba-Ahmed ya ce Buhari zai tafi da kuri’unsa.

Kara karanta wannan

‘Danuwan Tsohon Gwamna Ya Fadawa Duniya Wanda Wike Yake Goyon Baya a Boye

Na yarda da kai - Salihu Yakasai

‘Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya yarda da ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na jam’iyyar LP a nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake magana a Twitter, Salihu Tanko Yakasai ya ce jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari za ta zo ta farko a jihar Kano a zaben bana.

NNPP.
‘Dan Takarar NNPP a 2023 Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Salihu Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yana ganin Atiku Abubakar da PDP za su zo na biyu yayin da Bola Tinubu zai zo na uku a jam’iyyar APC.

‘Dan takarar, bai yi maganar yadda za ta kaya da jam’iyyar adawa ta LP a 2023 ba. Za a fahimci yana hasashen babban zabe ne ba na Gwamna ba.

Yakasai wanda ya yi aiki da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya nuna jam’iyyar APC tana rasa farin jini a dalilin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Maganar Salihu Tanko Yakasai

“Na yarda dari bisa dari. Hasashena shi ne NNPP za ta zo ta farko, PDP kuma ta biyu sai kuma APC ta zo ta uku daf a bayanta.
Domin jam’iyyar APC ta na cigaba da kara bakin jini a Kano har ta kai jam’ian gwamnatin jiha su na sukar gwamnatin tarayya.
Su na yin haka domin ceton kan su a zaben Gwamna."

- Salihu Tanko Yakasai

Akwai wasu manya a APC da ba su gamsu da Asiwaju Tinubu ya karbi shugabanci kasar nan ba, Salihu Lukman ne aka rahoto yana wannan maganar,

A cewar shugaban na APC, wadannan mutane ne suka nemi a tsaida Godwin Emefiele, Dr. Goodluck Jonathan ko kuma Ahmad Lawan a jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel