‘Danuwan Tsohon Gwamna Ya Fadawa Duniya Wanda Wike Yake Goyon Baya a Boye

‘Danuwan Tsohon Gwamna Ya Fadawa Duniya Wanda Wike Yake Goyon Baya a Boye

  • Isaac Fayose ya yi magana a shafinsa na Facebook, ya fasa-bakin yadda zaben 2023 zai kasance
  • ‘Danuwan fitaccen ‘dan siyasar ya fadawa mutanen Peter Obi hanyar lashe zaben shugabancin kasa
  • A nan ne Fayose ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike yana yi wa Bola Tinubu aiki a jihar Ribas

Ekiti - Kani ga tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose watau Isaac Fayose, ya na ikirarin Nyesom Wike bai tare da jam’iyyarsa a babban zabe.

A ranar Laraba, Vanguard ta rahoto Isaac Fayose yana cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, yana goyon bayan takarar Asiwaju Bola Tinubu.

Da yake bayani da fashin-baki a kan zaben 2023 a shafinsa na Facebook, Isaac Fayose ya ba magoya bayan Peter Obi shawarar yadda za su lashe zabe.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Fayose ya jero jihohin da ya ce ya kamata jam’iyyar LP da magoya bayanta su maida hankali a kansu domin ‘dan takaransu ya iya zama shugaban kasa.

Maganar Isaac Fayose a Facebook

“Kusan zabe ya karaso, akwai bukatar jam’iyyar LP da kungiyoyin da ke goyon bayan Peter Obi su karkata zuwa jihohin tsakiyar Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Musamman Filato da Benuwai da kuma jihohin Ondo, Legas, Kaduna, Taraba. Wadannan wurare ne da za sui ya samun kuri’u masu yawa.
Nyesom Wike
Nyesom Wike wajen kamfe Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Wike yana tare da APC?

Ya kamata a samu kuri’u masu yawa sosai a yankin Kudu maso gabas. A Kudu maso kudu kuwa Nyesom Wike yana yi wa Bola Tinubu aiki.
Akwai yaudarar mutane da ake yi da kyau a Akwa Ibom, Okowa ya shirya yaki a jihar Delta, sai an yi aiki a kan Bayelsa, za ayi nasara a Edo.

Kara karanta wannan

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

Tinubu yana wasa da hankalin mutane a Kudu maso yamma, abin takaici, hakan yana tasiri.”

- Isaac Fayose

Kamar yadda Daily Post ta fitar da rahoto, akwai alamun cewa kanin jagoran na jam’iyyar PDP bai tare da shi, yana goyon bayan Peter Obi a 2023.

Rikicin Atiku da 'Yan G5

Sanannen labari ne cewa Gwamnan na Ribas bai goyon bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a 2023, a dalilin kin yarda a tsige Iyorchia Ayu.

Nyesom Wike da sauran Gwamnonin da ke cikin kungiyar G5 sun dage cewa sai shugabancin jam’iyyar PDP ya koma kudu domin ayi masu adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel