Shugaban APC Ya Tona Wadanda Suke Yakar Bola Tinubu Ta Bayan-Fage a Jam’iyya

Shugaban APC Ya Tona Wadanda Suke Yakar Bola Tinubu Ta Bayan-Fage a Jam’iyya

  • Shugaban jam’iyyar APC a Arewa ta yamma ya yi bayani a kan masu adawa da Asiwaju Bola Tinubu
  • Salihu Lukman ya ce wadanda ba su kaunar Tinubu ne suka jawo aka fito da tsarin takaita yawon kudi
  • ‘Dan siyasar yana ganin manufar tsare-tsaren da CBN ya fito da shi, shi ne APC ta sha kashi a zaben 2023

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Salihu Lukman ya ce masu goyon Ahmad Lawan ne ke yakar Bola Tinubu.

A rahoton The Cable a ranar Talata, an fahimci wadanda suka so Ahmad Lawan ya zama ‘dan takaran shugaban kasa ba su tare da Bola Tinubu har yau.

Salihu Lukman ya ce mutanen da suka so su tsaida shugaban majalisar dattawa a matsayin ‘dan takaran 2023 ne suka fito da tsare-tsare ta hannun CBN.

Kara karanta wannan

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

Shugaban na APC yana zargin cewa haushin rashin samun takara ya jawo mutanen nan suka kawo tsarin takaita yawon kudi da jama’a suke kuka a kai.

Ba su son Tinubu a APC - Lukman

A matsayinsa na daya daga cikin manya a jam’iyya mai-ci, Lukman ya nuna Tinubu ba shi ne ‘dan takaran da wasu manya suka so ya samu tutan APC ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Kamfen Bola Tinubu a Ekiti Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

“Akwai wasu manya a APC da ba su natsu da yiwuwar Asiwaju Tinubu ya zama sabon shugaban kasar tarayyar Najeriya ba.
Wadanda suka gagara tsaida Emefiele, Jonathan ko Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takara ne suka fito da tsarin takaita kudi.
Wadannan mutane sun yi haka ne domin a bata jam’iyyar APC da takarar Asiwaju Tinubu
Yadda Asiwaju Tinubu ya samu tikitin APC duk da makarkashiyarsu, haka Tinubu zai zama shugaban kasa in Allah ya so.”

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

- Salihu Lukman

Burin jama'a zai cika a mulkin Tinubu

Vanguard ta rahoto Lukman yana cewa tun farkon kafa APC, wannan shi ne burin da ake da shi.

‘Dan siyasar ya bayyana cewa idan tsohon Gwamnan na Legas ya yi nasarar kafa gwamnati a karkashin jam’iyyar APC, burin ‘Yan Najeriya zai cika.

Taron Buhari da Gwamnoni

An ji labarin fasa zaman shugaban kasa da Gwamnoni amma ya hadu da Gwamnan babban banki, Godwin Emiefele, da shugaban EFCC kan shirin zabe.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da Farfesa Ibrahim Gambari su na wajen tattaunawar, an kuma hangi shugaban hafsoshin tsaro na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel