Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

  • Ministan ayyuka da gidaje ya ce Jam’iyyar APC za ta doke ‘Yan adawa kamar yadda aka yi a 2019
  • Raji Babatunde Fashola yake cewa Jam’iyyar PDP ba ta iya doke APC a lokacin da take da karfi sosai ba
  • Ganin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun koma LP da NNPP, Ministan ya ce Bola Tinubu ne zai ci zabe

Lagos - Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Raji Babatunde Fashola yana da tabbacin jam’iyyar APC za ta lashe zabe mai zuwa da za a shirya.

A ranar Litinin, 6 ga watan Fubrairu 2023, Punch ta rahoto Raji Babatunde Fashola yana cewa jam’iyyarsu ta APC mai mulki za tayi galaba a zabe.

A halin yanzu saura kusan kwanaki 20 a shirya zaben sabon shugaban kasa a duka jihohin Najeriya.

Tsohon Gwamnan na jihar Legas yake cewa siyasa harka ce ta yawan jama’a, kuma ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai rike da mulki sun fahimci wannan.

Kara karanta wannan

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

Ministan tarayyar ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka zanta da shi a wani shirin siyasa da ake yi a daren talata a gidan talabijin Channels.

'Yan APC
'Yan APC a Katsina Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rantsuwa ake jira kurum - Fashola

“Saura ‘yan kwanaki kadan ayi zabe yanzu, bai kai makonni uku ba. Mu na tafiya da karfinmu. Jam’iyya APC za ta lashe zaben nan.
Mu na hangen bikin rantsuwa ne. Mun san cewa takara ce kuma ‘yan adawa su na bayanmu sosai. Bari in fada maku dalilin fadan haka.
Manyan jam’iyyun hamayya a yau na LP, NNPP da PDP duk su na tare a zaben 2019. Kuma duk da haka mun ba su tazarar miliyan uku."

- Raji Babatunde Fashola

Sai dai idan daga wajen Najeriya za a dauko mutane

Kamar yadda aka fitar da labarin a Nairaland, jagoran na APC yana cewa babu yadda za ayi yanzu da ‘yan adawa suka kara rabuwa, su iya doke su a zabe.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fadawa Katsinawa Adadin Kuri’un da Yake so su ba Tinubu a zaben 2023

Idan dai ba za a tattaro wasu mutane daga wajen Najeriya ba ne, Babatunde Fashola yana ganin Bola Tinubu da Jam’iyyar APC sun gama samun nasara.

A tattaunawar da aka yi da shi, babban Ministan ayyuka da gidajen ya nuna farin cikinsa kan yadda mafi yawan jama’a suka damu da zaben na bana.

Kiran Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai

Tun da PDP tayi shekaru 16 a kan mulki, an ji labari Janar Tukur Buratai ya ce akwai bukatar mutanen kasar nan su ba jam’iyya APC dama ta zarce a 2023.

Idan APC ba ta tabuka komai ba, tsohon hafsun ya ce ayi waje da ita. Amma a yanzu yana ganin zai yi kyau a cigaba da bin turbar Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel