Kashim Shettima Ya Je Fadar Sarkin Daura, Ya Kashewa Takarar Atiku Kasuwa a PDP

Kashim Shettima Ya Je Fadar Sarkin Daura, Ya Kashewa Takarar Atiku Kasuwa a PDP

  • Sanata Kashim Shettima ya roki Daurawa su zabi Jam’iyyar APC mai-ci a zabe mai zuwa da za ayi
  • ‘Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasan na APC ya soki takwaransa, Atiku Abubakar
  • Kashim Shettima ya ce duk da Atiku ‘Dan Arewa ne, ba a amfana da shi yayin da yake Aso Villa ba

Katsina - ‘Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a APC, Kashim Shettima ya yi kira ga mutane su guji zaben Atiku Abubakar a PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sanata Kashim Shettima ya yi wannan magana na ne a lokacin da ya ziyarci Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Farouk.

Kashim Shettima ya kamanta zaben ‘dan takarar jam’iyyar PDP da cin amanar shugaba Muhammau Buhari wanda ya fito daga garin Daura.

Dalilin da tsohon Gwamnan na Borno ya bada shi ne, a cewarsa a lokacin da Atiku Abubakar ya samu mulki, bai taimakawa yankinsa na Arewa ba.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Kwankwaso Zai Janye Wa Atiku Takara? Sabbin Bayanai Sun Fito Ana Gab Da Zaben 2023

Abdul Danja, daya daga cikin matasan da ke goyon APC da Bola Tinubu ya daura wannan bidiyo.

Shettima yake cewa ba za a iya nuna mutum akalla takwas wadanda Atiku ne ya taimaka masu a lokacin da ya rike mataimakin shugaban kasa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kashim Shettima Ya Je Fadar Sarkin Dutse
Kashim Shettima tare da Marigayi Sarkin Dutse Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Kira ga al'umma - Kashim Shettima

"Mu na kiran al’umma musamman na jihar Katsina, musamman na jihar Borno, musamman na Daura, Wallahi idan ba ku yi APC ba, kun ci amanar Buhari, kun ci amanar kasa.
Hakika ‘naka na ka ne’, nakan da ya san cewa shi na ka ne, shi ne na ka. Amma nakan da shi aljihunsa kurum ya sani ba na ka ba ne.
Atiku ya yi mataimakin shugaban kasa na shekaru takwas, ya kirga ayyuka takwas da ya kawowa Arewa (ba Katsina ba), ya kirga takwas.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Ya kirga mutane takwas da ya gina a Arewa, mu yi abin da ya dace, mulkin nan daga Allah ne."

- Kashim Shettima

Hausawa, Barebari da Fulani 'yanuwa ne

‘Dan siyasar ya kuma fadawa masarautar kasar Daura cewa babu Fulani da Barebari ‘yanuwan juna ne, ya ce shi karon kan shi yana da jinin Fulani.

Sanatan na Borno ta tsakiya ya ce irinsu Muhammadu Buhari, Shehu ‘Yaradua da Mamman Daura duk Katsinawa ne da suke da jinin Bare-bari.

2023: Lokacin Yarbawa ya yi

A jiya aka samu labari Gwamnan Ondo yace ya yarda Najeriya tana cikin ha’ula’i a mulkin gwamnatinsu, ya fadi wanda zai ceci al’ummar kasar nan.

Rotimi Akeredolu yana goyon bayan Bola Tinubu, bai taba boye manufarsa na ganin shugaban kasa ya fito daga Kudu bayan Muhammadu Buhari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel