Abin da Zai Faru Idan Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamnan APC

Abin da Zai Faru Idan Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamnan APC

  • Gwamnan jihar Ondo ya ce Bola Tinubu zai ceci kasa idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya
  • Rotimi Akeredolu yana fatan burin da suke da shi na samun Bayarabe a Aso Rock zai tabbata a 2023
  • Shugaban APC ya ankarar da mutane cewa akwai bukatar ‘Dan Kudu ya karbe shugabancin kasa

Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce Najeriya za ta cigaba a karkashin jagoracin Bola Tinubu mai takara a jam’iyyar APC.

The Cable ta rahoto Rotimi Akeredolu ya na cewa mutane su zabi Bola Tinubu domin ganin burinsu na maidawa ‘Yan yankin Kudu mulki ya tabbata.

Mai girma Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen wani taro da jam’iyyar APC ta shirya a mazabar Arewacin jihar Ondo domin samun nasara a zabe.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Gwamnan ya nuna burinsu shi ne a samu shugaban kasa daga Kudancin Najeriya bayan Muhammadu Buhari ya cika wa’adinsa a karagar mulki.

Tinubu zai kawo cigaba

Akeredolu ya ce tsohon Gwamnan na Legas ne zai iya gyara Najeriya, ganin halin da ta ke ciki a yau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Asiwaju Ahmed Bola Tinubu mutum ne wanda an jarraba shi, kuma bai bada kunya ba.
Ya yi Gwamnan Legas, kuma mun san yadda ya gyara jihar. Ina iya tabbatar maku da cewa Najeriya za ta cigaba a karkashin mulkin Tinubu.”

- Rotimi Akeredolu

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kiran da Shugaban APC ya yi

A matsayinsa na shugaban jam’iyya na reshen Ondo, jaridar ta ce Ade Adetimehin ya yi makamancin wannan kira ga magoya bayan Tinubu da APC.

Shi ma Ade Adetimehin ya fadawa mutane cewa su tallata jam’iyyar APC a jihar Ondo domin lokaci ya yi da Bayarabe zai karbi shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon Hafsun Sojoji, Buratai Ya Bayyana ‘Dan Takaran da Yake yi wa Aiki a 2023

Bayan Tinubu, shugaban jam’iyyar ya roki jama’a su zabi ‘yan takaran APC da ke neman kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai da na dokoki.

Guardian ta ce bayan taron, Adetimehin ya karbi mutane fiye da 500 da suka fice daga jam’iyyar PDP a garin Akoko, yanzu sun yi alkawarin taimakon APC.

A wajen gangamin, karamin Ministan sufuri, Ademola Adegoroye ya tallata takarar ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, yake cewa a zabi duk wadanda aka ba tikiti.

Wike yana tare da APC - Fayose

Bola Tinubu ne wanda Gwamna Nyesom Wike yake yi wa aiki a zaben Shugaban Kasa. An samu labari cewa Isaac Fayose ya bayyana haka a Facebook.

‘Dan uwan fitaccen siyasar ya ce magoya bayan Peter Obi da 'Yan jam'iyyar LP su yi harin kuri’un Filato, Benuwai, Kaduna, da Taraba a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel