Maja: Atiku Ya Aiko Tsoffin Shugabanni Su Roki Kwankwaso, Buba Galadima

Maja: Atiku Ya Aiko Tsoffin Shugabanni Su Roki Kwankwaso, Buba Galadima

  • Sabbin bayanai sun fito game da yunkurin Atiku na rarrashin Kwankwaso ya janye masa takarar shugaban kasa
  • Buba Galadima, jigo a jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya bayyana manyan mutanen da Atiku ya tura gidan Kwankwaso
  • Tsohon makusancin Buhari ya ce har rumfar da Atiku ke kaɗa kuri'a a jihar Adamawa NNPP zata samu galaba

Buba Galadima, jigo a jam'iyyar NNPP ya ce ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya cigaba da tura manyan mutane su rarrashi Rabiu Kwankwaso, ya hakura da neman zama shugaban ƙasa.

Galadima, tsohon makusancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce Atiku ya wakilto mutanen ne domin su roki Kwankwaso ya hakura ya mara masa baya a zaɓe mai zuwa.

Buba Galadima.
Maja: Atiku Ya Aiko Tsoffin Shugabanni Su Roki Kwankwaso, Buba Galadima Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jigon jam'iyya mai kayan marmari ya bayyana haka ne a cikin shirin Daily Politics na kafar Talabijin ɗin Trust Tv, inda ya kara da cewa NNPP zata yi nasara har a rumfar zaɓen Atiku.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Goyi Bayan Buhari, Ya Fallasa Manufar Canja Kuɗi Ana Gab da Zaben 2023

A kalamansa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Zamu lallasa Atiku a karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa. Atiku ba ya cikin tseren takara, eh zamu iya cewa akwai shi a kuri'a amma ba ɗan takarar gaske bane, ta ya zai ci zaɓe, ta ina?"
"Atiku na amfani da shugabannin Addini su roki Kwankwaso ya hakura ya janye masa, Atiku ya yi amfani da tsoffin shugaban kasa da manyan masu faɗa aji domin su lallashi Kwankwaso."
"Atiku ya dauko Sarakuna, ya kashe biliyoyin naira wajen jawo ra'ayinsu su je su rarrashi Kwankwaso ya janye ya koma bayansa. Ya yi amfani da kungiyoyin manyan arewa don su yi hira da yan takara daga baya su ce Atiku ya fi cancanta."

Buba Galadima ya caccaki kungiyoyin manyan arewa inda ya ce sun fi su zama cikakkun 'yan arewa kuma dattawa na gaske.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Hadewar NNPP da Atiku

Atiku ya tura Malamai wurin Kwankwaso

"Mune cikakkun 'yan arewa fiye da su, Kwankwaso ɗan Kano ne ni kuma ɗan Gashuwa, ƙauyen mu na can cikin arewa tsundum saboda haka na fi su zama ɗan arewa kuma Dattijo."
"Kwanan nan Atiku ya aiko wasu manyan Malaman Addinin Musulunci su uku gidan Kwankwaso suka duƙa har ƙasa suna rokonsa ya janye."
"Muka kore su, Eh su waye su? Muna girmama Malunta amma idan suka cire rigar ilimi, zamu sa kananan yara su mana maganinsu."

- Galadima.

Idan baku manta ba, NNPP ta jaddada cewa Kwankwaso ba zai taɓa janyewa daga takarar shugaban kasa ba domin shi ne zai samu nasara, kamar yadda Guardian ta rahoto.

Obi zai ba da mamaki - Jigon LP

A wani labarin kuma An bayyana Dalilin Da Yasa Peter Obi Zai Samu Kuri'u da Yawa a Arewa a Zaben 2023

Ibrahim Abdulkarim, jigon jam'iyya LP, ya yi hasashen cewa ɗan takarar LP zai samu tulin kuri'u a arewa fiye da kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

A cewarsa, mazauna arewacin Najeriya zasu dangwala wa Obi ne saboda fusshin da suka yi da yan siyasa sakamakon halin da aka jefa su a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel