Zabe Saura Kwana 18, Jagorori a APC Sun Rabu da Tinubu, Sun Bi Atiku/Okowa

Zabe Saura Kwana 18, Jagorori a APC Sun Rabu da Tinubu, Sun Bi Atiku/Okowa

  • Jam’iyyar APC ta rasa wasu daga cikin Shugabannin mazabun ta kananan hukumomin Delta
  • ‘Dan takaran Gwamnan PDP a zaben 2023, Sheriff Oborevwori ya karbi wadanda suka sauya-shekar
  • Shugabannin za su marawa takarar Atiku Abubakar da Sheriff Oborevwori baya a maimakon APC

Delta – Shugabannin mazabu masu-ci su takwas suka sauya-sheka daga jam’iyyar APC a jihar Delta, yanzu sun tsallaka zuwa PDP mai mulki.

Rahoton Vanguard na daren Laraba ya bayyana cewa wadannan shugabannin jam’iyya na mazabu duk sun yi murabus, sun bi jam’iyyar PDP.

‘Dan takaran Gwamnan jihar Delta a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori ne ya karbi tsofaffin shugabannin na APC a jiya.

Kamar yadda suka shaida da bakinsu, ‘yan siyasa sun yi alkawarin za su yi PDP da ‘yan takaranta aiki a mazabun da suka fito a zaben da za ayi.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Su wanene su ka bar APC?

An rahoto ‘yan siyasar su na cewa su da magoya bayansu duk sun yi watsi da jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda jam’iyyar APC ta rasa su ne: Sunday T. Oyabrade, Volvo Oyayefa, Ofene Emejor. Sannan akwai Bini Maxwell da Festus Godspower.

Ragowar sun hada da Egbe Angom, Justin Ogbomeniegha da kuma Timbo Zudegibe.

Taron PDP
Taron Atiku/Okowa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Sauya-shekar na nufin jam’iyyar PDP mai mulkin Delta ta kara karfi a mazabun Burutu, Bomadi, da Kudancin Warri a yankin Kudu maso kudu.

2023: Delta sai PDP

Masu sauya-shekar sun yaba da aikin Gwamna Ifeanyi Okowa, suka ce sun ga akwai bukatar su taimakawa jam’iyyar PDP ta kai ga nasara a 2023.

Bayan sun fice daga jam’iyyar, shugabannin mazabun sun ce babu wani abin da APC za ta iya yi a Delta, suka tabbatar da goyon bayansu ga PDP.

Kara karanta wannan

Kwana 20 Gabanin Zabe, Atiku Ya Yi Wa Tinubu Babbar Illa da Ka Iya Jawo Masa Rashin Nasara

Baya ga ‘yan APC, ‘yan takaran jam’iyyar APGA a Burutu, Demebide Pele da Hon Bibakefie Ebi sun bada sanarwar sauya-shekarsu gab da zabe.

Rahoton ya ce Rt Hon Sheriff Oborevwori ya karbi Hon. Efezhino Ilaye Thukson mai neman takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a inuwar ADP.

Wike yana tare da APC

Bola Tinubu ne wanda Gwamna Nyesom Wike yake yi wa aiki a zaben Shugaban Kasa. An samu labari cewa Isaac Fayose ya fadi haka a Facebook.

Isaac Fayose ya nuna jam'iyyar APC ta fara karfi a Ribas, sannan ya ce PDP za ta karbe Delta, yayin da ake hangowa jam'iyyar LP nasara a jihar Edo

Asali: Legit.ng

Online view pixel