Jam'iyyar APC Ta Gamu da Cikas a Edo, Mambobi 3,000 Sun Koma PDP

Jam'iyyar APC Ta Gamu da Cikas a Edo, Mambobi 3,000 Sun Koma PDP

  • Yayin da ya rage kwanaki 20 babban zabe, jam'iyyar APC mai mulkin ƙasa ta gamu da babban tasgaro a jihar Edo
  • Wasu manyan kusoshin APC da shugabanni sun tabbatar da sauya sheka zuwa APC a wurin taron yakin neman zabe a karshen mako
  • A cewarsu sun yi dana sanin zaben APC domin ba ta tsinana masu komai ba sai talauci da wahalhalu daban-daban

Edo - Sama da mambobi 3,000 na jam'iyyar APC a jihar Edo suka tattara kayansu suka koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a cewar rahoton jaridar Leadership.

Tsoffin mambobin APC sun sauya shekar ne a wuraren ralin PDP daban-daban a karshen makon nan a yankunan kananan hukumomin Ovia Southwest da Ovia Northeast.

Siyasar Najeriya.
Jam'iyyar APC Ta Gamu da Cikas a Edo, Mambpbi 3,000 Sun Koma PDP Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sun yaga katin mamban APC kuma sun lashi takobin tabbatar da PDP ta samu nasara manyan zabukan dake tafe musamman na watan Maris mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Da yawa daga cikin masu sauya sheƙar sun bayyana cewa sun gaji da wahalhalu da talauci wanda gwamnatin APC ta ƙaƙabawa mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kusoshin APC ta suka sauya sheƙa

Daga cikin masu sauya sheka zuwa PDP har da shugaban ƙungiyar Ciyamomin APC a ƙaramar hukumar Ovia ta kudu maso gabas, Sunday Kriya, da shugabannin APC na gundumomi da mataimakansu.

Daya daga cikin jiga-jigan masu sauya sheƙar, Mista Kumukumu, wanda ya yi hasashen APC zata riga rana faɗuwa a zaɓe mai zuwa, ya ce sun yi dana sanin zaben Idahosa a 2019.

Wani tsohon shugaban APC daga cikin masu sauya sheƙan, Sunday Kriya, ya lashi takobin kawo kuri'u 100 bisa 100 ga PDP da yar takarar majalisar tarayya, Omosede Igbinedion.

A cewarsa, Omosede ta tallafawa matasa kuma ta ba da kyautar kuɗaɗe ga mata lokacin da aka zabe ta a karon farko ta tafi wakilci majalisar wakilan tarayya.

Kara karanta wannan

Ta Rikice Wa Atiku, Gwamna Wike Ya Tuna Baya, Ya Faɗi Hukuncin da Zasu Yanke Wa PDP a Zaben 2023

A nata jawabin, Omosede ta yi alkawarin cewa zata ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar Edo idan aka zaɓe ta domin tabbatar da mutane sun amfana.

Allah Ku Yafe Mun, Tinubu Zai Dora Daga Inda Na Tsaya, Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya kara tabbatar da cikakken goyon bayansa ga Bola Tinubu a Ralin Katsina

Shugaban ƙasan ya kuma nemi ɗaukacin yan Najeriya da su yafe wa gwamnatin kura-kuran da ta yi amma su ci gaba da zaben jam'iyyar APC.

Duk da haka a cewar shugaban ƙasan, gwamnatinsa ta kawo ci gaba kuma ta samu nasarori na zamani a tsawon lokacin da ta kwashe a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel