Masu Lalurar Tabin Hankali Ne Kawai Za Su Zabi APC - Ayu

Masu Lalurar Tabin Hankali Ne Kawai Za Su Zabi APC - Ayu

  • Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya fadi rukunin wadanda za su zabi jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa
  • Ayu ya yi kira ga masu zabe da kada su yi asarar kuri'unsu a kan APC cewa zautattu ne kawai za su zabi jam'iyyar mai mulki a 2023
  • Ya ce ana kan tattaunawa da fusatattun mambobin PDP domin yin sulhu kafin ranar 25 ga watan Fabrairu

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyorchia Ayu, ya bukaci yan Najeriya da kada su yi asarar kuri'unsu wajen zabar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Da yake magana a ranar Talata yayin gangamin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar PDP a jihar Benue, Ayu ya yi ikirarin cewa masu lalurar tabin hankali ne kawai za su zabi APC, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Jiga-jigan APC
Masu Lalurar Tabin Hankali Ne Kawai Za Su Zabi APC - Ayu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ayu ya ce:

"Dukkaninku kun san cewa kun sha wahala a kasar nan a shekaru takwas da APC ta yi tana mulki, mutum mai lalurar tabin hankali ne kawai zai zabi APC. Kada ku yi asarar kuri'arku."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ayu ya magantu kan rikicin PDP

Da yake magana kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, Ayu ya ce ana nan ana kokarin sulhu kuma cewa shugabancin PDP tana tattaunawa da fusatattun 'ya'yan jam'iyyar, rahoton Thisday.

Ya ce:

"Jam'iyyar bata rabu ba. Akwai 'ya'yan jam'iyya kadan da suka fusata. Muna tattaunawa da su. Muna so mu tabbatar da ganin sun dawo sannan sun yi aiki tare da mu. Mako daya iya isa ya sauya komai. Abubuwa na ta gudana kuma ina so na tabbatar maku cewa za mu dawo da kowa."

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP Ta Roki Yan Najeriya Da Su Zabi Atiku Saboda Dalili Daya

Dan Allah ka dawo gida, Ayu ya roki Gwamna Samuel Ortom

Ya kuma roki gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da ya shigo kamfen din PDP sannan ayi harkoki da shi don nasarar PDP a zaben shugaban kasa.

"Ina rokon kanina, Gwamna Ortom da ya dawo sannan ya hada hannu da mu don mu yi yaki wajen ceto Najeriya. Gwamna Ortom bai da wurin zuwa, gidan da yake da shi kawai shine PDP kuma a duk lokacin da ya zo, za mu fi kowa farin cikin tarbarsa da daukacin gwamnonin PDP.
"Muna so dukkanin yan takararmu, dukkanin gwamnoninmu su kasance tare da mu saboda idan muka bari APC ta yi nasara a zaben nan, za ku yi danasani."

Ku yi waje da APC a zaben shugaban kasa, Saraki ga yan Najeriya

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bukaci yan Najeriya da su tabbata sun mallaki katin zabensu don yin waje da APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel