Zaben Shugaban Kasa: Ku Mallaki Katin Zabenku Sannan Ku Yi Waje Da APC – Saraki Ga Yan Najeriya

Zaben Shugaban Kasa: Ku Mallaki Katin Zabenku Sannan Ku Yi Waje Da APC – Saraki Ga Yan Najeriya

  • Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya bayyana ra'ayinsa kan yadda sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 ka iya kasancewa
  • Yan kwanaki kafin zaben, tsohon dan majalisar kuma jigon PDP ya bukaci yan Najeriya da su yi waje da APC wacce ta jefa kasar a cikin wahala
  • Saraki ya yi kira ga masu zabe da su guji zanga-zanga kowace iri ce amma su mallaki katunan zabensu sannan su sauke hakkinsu na yan kasa

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana yadda yan Najeriya za su iya aiwatar da hakokinsu na yan kasa a babban zaben shugaban kasa da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter kuma Legit.ng ta gani a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, Saraki ya bukaci yan Najeriya da su guji ta da rikici ko wani iri ne, musamman zanga-zanga.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

Saraki ya kuma yi kira ga yan kasar da su mallaki katunan zabensu PVC don yin waje da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wacce ta jefa al'umma cikin wahala na tsawon shekaru takwas.

Bukola Saraki
Zaben Shugaban Kasa: Ku Mallaki Katunan Zabenku Sannan Ku Yi Waje Da APC – Saraki Ga Yan Najeriya Hoto: Bukola Saraki
Asali: Facebook

Saraki ya ba yan Najeriya muhimmin aiki gabannin zaben shugaban kasa na 2023

Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) ya wallafa a Twitter:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan zaben na 2023 na kada kuri'ar rashin karfin gwiwa a gwamnatin APC ne a matakin rashin tsaro, tsananin talauci da rashin sanin makamar aiki a bangaren zaman takewa da tattalin arzikinmu
"Yayin da zabe ya saura kwanaki 19, katin zabenku shine zanga-zangar da za ku yi a yaunzu. Duk wani nau'i na zanga-zanga a wannan lokacin ba zai yi tasiri ba.
"Kun jure wahala tsawon shekaru 8 da suka gabata, yan kwanaki suka yi saura."

Kara karanta wannan

APC Ta Dage Kamfen Dinta Na Shugaban Kasa a Wata Jihar Kudu, Ta Fadi Dalili

APC ta dage kamfen dinta a jihar Oyo saboda karancin man fetur da sabbin kudi

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar APC ta dage gangamin kamfen dinta na shugaban kasa a jihar Oyo saboda zanga-zanagr da ke gudana a jihar kan karancin takardun sabbin naira da man fetur.

Al'ummar Najeriya na fama da matsi sakamakon karancin sabbin kudi da matsalar man fetur wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel