2023: Magoya Bayan PDP Sun Roki Yan Najeriya Da Su Ceto Kasar Ta Hanyar Zabar Atiku

2023: Magoya Bayan PDP Sun Roki Yan Najeriya Da Su Ceto Kasar Ta Hanyar Zabar Atiku

  • Yan kwanaki kafin zabe, an yi kira ga yan Najeriya da su zabi Atiku Abubakar a matsayin magajin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
  • Kungiyar 'WAZIRIN Adamawa Movement' ta ce ya zama dole a zabi dan takarar na PDP domin ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki
  • Kungiyar ta magoya bayan PDP ta ce yanzu ba maganar jam'iyyar siyasa ake yi ba, magana ce ta hana Najeriya durkushewa

Bauchi - Yayin da babban zaben kasar ke kara gabatowa, wata kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar mai suna 'WAZIRIN Adamawa Movement' ta gana da masu ruwa da tsaki a fadin jam'iyyun siyasa a Bauchi kan yadda za su tabbatar da ganin ya yi nasara.

A cewar shugaban kungiyar, Abubakar Kari, zabar Atiku domin ya jagoranci Najeriya ba abu ne na jam'iyya ba a yanzu illa fafutukar ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki a yanzu, AIT ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Zai Girgiza Yan Najeriya

Atiku Abubakar
2023: Magoya Bayan PDP Sun Roki Yan Najeriya Da Su Ceto Kasar Ta Hanyar Zabar Atiku Hoto: AIT
Asali: UGC

Wannan shine matsayin wasu manyan yan siyasare Bauchi, da aka tara daga dukkanin jam'iyyun siyasa a fadin kananan hukumomi 20 na jihar.

Atiku Abubakar zai hana kasar durkushewa idan ya gaji Buhari, Kungiya

Sun hadu don tattauna lamuran da ke kewaye da zaben 2023 kan dalilin da yasa akwai bukatar a zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar People’s Democratic party, Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa na gaba don ceto kasar da ke hanyar durkushewa a cewarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar ta bukaci yan Najeriya da su ajiye siyasa a gefe sannan su yi nazari sosai kan masu neman zaben shugaban kasa kafin su kada kuri'arsu.

Kungiyar ta bugi kirji cewa Atiku Abubakar na PDP shine mutumin da ya fi cancanta da shugabancin Najeriya.

Kungiyar ta dage cewa a yanzu da siyasar kasar ke kara zafi, yayin da jam'iyyun siyasa da magoya bayansu ke kokarin tallata kansu, zabar shugaba irin Wazirin Adama shine ya fi muhimmanci.

Kara karanta wannan

2023: Da Gaske Atiku Da Peter Obi Za Su Yi Maja? Labour Party Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

Yan Najeriya sun yanke shawarar zaben Atiku, PDP

A halin da ake ciki, Kola Ologbondiyan, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce yan Najeriya sun yanke shwarar zabar Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

A wani jawabi da ya saki a ranar Juma'a,Ologbondiyan ya yi zargin cewa akwai wani yunkuri da ake na amfani da rikici wajen tarwatsa zaben, jaridar The Cable ta rahoto.

Jam'iyyar APC ta fara bi gida-gida tana yi wa Tinubu kamfen a Nasarawa

A wani labarin, mun ji cewa kungiyoyin goyon bayan APC sun fara bi gida-gida suna yi wa Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima kamfen a jihar Nasarawa.

Wannan na daga cikin kokarinsu na ganin jam'iyya mai mulki ta lashe kujerar Shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel