Gungun ‘Yan Siyasa Daga Jihohi 11 Sun Yi wa Takarar Atiku/Okowa Mubaya’a

Gungun ‘Yan Siyasa Daga Jihohi 11 Sun Yi wa Takarar Atiku/Okowa Mubaya’a

  • Kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta zauna, ta tsaida ‘dan takaranta a zaben 2023
  • Kakakin CUPP a Delta, Prince Henry Eze ya bada sanarwar za a goyi bayan Atiku Abubakar a jihohin Kudu
  • Eze ya nuna CUPP ta reshen Kudu maso gabas da Kudu maso yamma za su marawa PDP baya ne

Delta - A ranar Alhamis, 26 ga watan Junairu 2023, gamayyar kungiyar jam’iyyun siyasa watau CUPP, ta bada sanarwa kan ‘dan takararta a zabe mai zuwa.

Vanguard ta rahoto cewa kungiyar CUPP tana goyon bayan takarar Alhaji Atiku Abubakar da abokin gaminsa, Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a PDP.

Kamar yadda aka bada sanarwa, wannan ita ce matsayar duka shugabannin kungiyar na rassan jihohin Kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Kakakin CUPP na Delta, Prince Henry Eze ya bada wannan sanarwa a yammacin Alhamis.

CUPP tana goyon bayan PDP

Da yake jawabi a garin Asaba a jiya, Prince Henry Eze ya ce shugaban sashen kungiyar mai zaman kan ta, Mr Ken Ikeh ya jagoranci mubaya’ar da aka yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ikeh ya ce ‘yan siyasar su na goyon bayan tikitin Atiku-Okowa a zabe mai zuwa ne bayan la’akari da manufofin wadanda suka kafa kungiyar ta CUPP tun farko.

Taron PDP
Taron Atiku/Okowa a Abakaliki Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tribune ta ce Kakakin kungiyar ya kara da cewa halin da Najeriya ta samu kan ta a yau, ya tursasawa CUPP daukar wannan matsaya a jihohin yankunan.

A al’ada, kungiyar siyasar ta na duba wadanda suka tsaya neman takaran shugaban kasa, sai ta fito da wanda take ganin ya fi cancanta da mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha romo, Kwankwaso ya karye a Arewa, 'yan NNPP 170,000 sun koma PDP a wata jiha

Abin da CUPP ta duba

Daga cikin abin da aka duba shi ne mutanen kudancin Najeriyan sun dade su na kiran a canza fasalin tattali, wanda hakan yana cikin manufofin Atiku.

"Atiku ya na goyon bayan a canza fasalin kasa, kuma ya yi alkawarin rage karfin tarayya, ya karawa jihohi karfi
Atiku ya yi mataimakin shugaban kasa, shi ya fi kowa sanin aiki a cikin masu neman shugabancin Najeriya.
Baya ga haka, takararsa tare da Gwamna Ifeanyi Okowa ta cika sharudan tikiti na Musulmi da kuma Kirista.
Dauko Dr. Okowa a matsayin abokin gami da ‘dan takaran na PDP ya yi, ya nuna yadda ya ke kaunar kabilar Ibo."

- Prince Henry Eze

Taron 'Yan Kungiyar I Am Change

Rahoto ya ce a ranar Alhamis, Kungiyar I Am Change ta shirya taro inda aka tattauna batun tsaro. Janar Abdulrahman Dambazau yana cikin masu jawabi.

Tsohon hafsun sojin ya ce siyasar addini, bangaranci da kabilanci da 'yan siyasar Najeriya suka fito da shi ya jawo rashin zaman lafiya da rabuwar kai.

Kara karanta wannan

APC Ta Ga Jama’a a Kamfe, Ta Ce Gwamnan PDP Ya Tattara Kayansa Daga Gidan Gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel