Mai Dakin Tinubu Za a Damkawa Mulki Idan Har Aka Zabi APC - Naja’atu Muhammad

Mai Dakin Tinubu Za a Damkawa Mulki Idan Har Aka Zabi APC - Naja’atu Muhammad

  • Naja’atu Muhammad ta na da ra’ayin cewa ko Bola Tinubu, ya lashe zabe, ba shi zai yi mulki ba
  • ‘Yar siyasar ta na ganin nasarar jam’iyyar APC yana nufin an damkawa matar Tinubu madafan iko
  • Tsohuwar ‘yar jam’iyya mai-mulkin ta na zargin cewa Asiwaju Bola Tinubu bai da isasshen lafiya

Abuja - Naja’atu Muhammad ta bayyana cewa idan Bola Tinubu ya yi nasara a zaben shugaban kasa, ya dare kan mulki, to ba shi zai rike madafan iko ba.

A wata hira da aka yi da shahararriyar ‘yar siyasar a gidan talabijin na AIT, Naja’atu Muhammad ta ce nasarar APC tana nufin an zabi mai dakin Bola Tinubu.

‘Yar siyasar tana cigaba da yin karin-haske ne a kan dalilin da ya sa ta fice daga jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

“A wannan yanayin, masu dagewa a kan neman mulki su na tura shi ne kurum, sun san su za su fi kowa cin moriya. Shi yana nan tamkar gunki.
Matarsa ce za ta rika shugabancin, ita za ta jagoranci kasar nan tare da sauran masu makalkale masa, a wurina ma ba su kaunar Asiwaju (Tinubu)
Domin kuwa ba za ka dauko mara lafiya, ka ba shi matsayin shugabanci ba. Wasu irin mutane ne mu? Wannan abin zai dawo ya ci mu gaba daya.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Naja’atu Muhammad

Tinubu
Tinubu da manyan APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

The Cable ta bibiyi hirar da aka yi da tsohuwar jigon ta APC, ta kawo abin da ya sa ta koma goyon bayan Atiku Abubakar mai takara a jam’iyyar adawa ta PDP.

Zargin da Naja’atu Muhammad take yi shi ne Atiku Abubakar ya na da manufofi, akasin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin APC, Aka Ba Shi Takara - Najaatu Mohammed

Tinubu bai iya tunani - Naja'

Na duba zabin da nake da shi a APC, za a je taro amma Asiwaju bai iya tunani da kyau. Na zauna da shi na awa biyu, amma duk barci kurum yake sharararwa.
Ka na tambayarsa wani abin, shi yana yi maka maganar wani abin dabam gaba daya. Me za ka samu da za ka yi sadaukar da mutum miliyan 200 a Najeriya?”

- Naja’atu Muhammad

Mai dakin ‘dan takaran shugaban kasar ita ce, Remi Tinubu wanda tun Mayun 2011, Sanata ce mai wakiltar jihar Legas ta tsakiya a majalisar dattawan kasar.

Ko da tsohon Gwamnan Musulmi ne, Sanata Remi Tinubu babbar Fasto ce a cocin nan na RCCG, ta rike uwargidar jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007.

'Yan takaran Gumsu Abacha

Rahoto ya zo maku cewa ‘Diyar tsohon Shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha ta ce a 2023, Kano sai Muhammad Abacha, a Katsina kuma sai Lado Danmarke.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Gumsu Abacha ta bayyana dalilinta na goyon Muhammad Abacha da Lado Danmarke a PDP, amma a zaben Shugaban kasa tana tare da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel