Mai Dakin Gwamnan APC Ta Yi Alkawarin Goyon Bayan ‘Yan Takaran Jam’iyyar PDP

Mai Dakin Gwamnan APC Ta Yi Alkawarin Goyon Bayan ‘Yan Takaran Jam’iyyar PDP

  • Gumsu Sani Abacha ta fadi dalilinta na goyon bayan wasu ‘Yan takaran Jam’iyyar adawa a 2023
  • ‘Diyar tsohon Shuaban kasar ta ce ‘danuwanta da surukinta suke neman Gwamna a Kano da Katsina
  • Kusancin Gumsu Abacha da APC ba zai hana ta goyon Muhammad Abacha da Lado Danmarke ba

Yobe - Gumsu Sani Abacha ta shaidawa mabiyanta cewa a zaben 2023, za tayi abin da ake kira wanke da shinkafa a siyasar Najeriya.

Hajiya Gumsu Sani Abacha ta bayyana haka a shafinta da ke dandalin sada zumunta na Twitter a ranar Talata, 24 ga watan Junairu 2023.

Duk da tana auren Gwamnan Yobe, kuma tana goyon bayan APC a babban zabe, Gumsu Abacha tana tare da wasu ‘yan takara a PDP.

Mai gidanta, Mai Mala Buni yana cikin manyan kusoshin APC a Arewacin Najeriya, kuma da alama tana goyon bayan Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Fallasa ‘Mugun Shirin’ da Tinubu Yake Kullawa

Wake da shinkafa a 2023

Hakan ba zai hana diyar tsohon shugaban Najeriyar ta marawa jam’iyyar hamayya ta PDP a zabukan Gwamnonin Kano da na Katsina ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan Baiwar Allah ta ce alakar jini ya fi kowane, saboda haka za ta mara baya ga ‘danuwanta da kuma surukinta ne a jihohin nan biyu.

Gumsu Abacha
Gumsu Abacha tana tare da PDP da APC Hoto: pulse.ng da @G_sparking
Asali: UGC

Meya hada Gumsu da PDP?

Muhammad Abacha ne yake takarar Gwamnan jihar Kano a PDP, shi ma Sanata Lado Danmarke yana neman Gwamnan Katsina a zaben bana.

Muhammad Abacha yana cikin ‘ya ‘yan Marigayi Sani Abacha, kamar Danmarke, tun a zaben 2011 ya yi burin zama Gwamnan Kano a CPC.

Shi kuma Lado Danmarke kwararren ‘dan siyasa ne wanda ya rike Shuaban karamar hukumar, ‘dan majalisar wakilai da Sanata duk a PDP.

Kara karanta wannan

Gungun ‘Yan Siyasa Daga Jihohi 11 Sun Yi wa Takarar Atiku/Okowa Mubaya’a

Danmarke mai shekara 61 a Duniya yana auren ‘diyar tsohon shugaban kasa, Zainab Abacha.

Ga masu bukatar su sani kuma su fahimta. Ina goyon bayan jam’iyyar PDP a jihar Kano da jihar Katsina saboda jini ba wasa ba ne.
‘Dan takaran PDP a Kano, yaya na ne, sannan ‘dan takaran PDP a Katsina, mijin ‘yaruwa ta ne.

- Gumsu Sani Abacha

Kashim Shettima ya hadu da Ayo Fayose.

An samu rahoto cewa take-taken Kashim Shettima sun nuna ya na kokarin amfana da rikicin cikin gidan PDP a Ekiti, ya hadu da Ayo Fayose.

Jagoran na APC da mutanensa sun taka zuwa gidan Fayose a Abuja. Dama tun ba yau ba ake ta kai ruwa-rana da tsohon Gwamnan a jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel