Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin APC, Aka Ba Shi Takara - Najaatu Mohammed

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin APC, Aka Ba Shi Takara - Najaatu Mohammed

  • Naja’atu Mohammed ta zargi Bola Tinubu da rabawa Gwamnoni kudi da nufin samun tikitin Jam’iyyar APC
  • Tsohuwar Darektar kwamitin neman shugaban kasar ta na ganin Yemi Osinbajo ya fi cancanta da yin takara
  • Tsohuwar ‘yar siyasar ta ce Gwamnonin APC suna so Tinubu ya rike masu kai, suyi wasa da wutsiyar maciji

Abuja - Tsohuwar ‘yar kwamitin neman shugaban kasa a APC, Naja’atu Mohammed tayi bayanin abin da ta sani a kan samun takara Bola Tinubu.

This Day ta rahoto Naja’atu Mohammed tana mai cewa da dukiya ne Bola Tinubu ya yi amfani wajen samun goyon bayan Gwamnonin jihohin APC.

‘Yar siyasar tana zargin kudi sun yi tasiri a zaben tsaida gwanin ‘dan takaran shugaban kasa a APC, ta bayyana abin da ya faru da abin kunya

Kara karanta wannan

APC Ta Ga Jama’a a Kamfe, Ta Ce Gwamnan PDP Ya Tattara Kayansa Daga Gidan Gwamnati

Hajiya Naja’atu Mohammed ta ce kataborar da ‘dan takaran na jam’iyyar APC yake yi a wajen yawon kamfe, a sakamakon rashin cikakken lafiya ne.

Osinbajo ya fi Tinubu cancanta

Tsohuwar ‘yar APC take cewa duba da rashin lafiyar Tinubu, kyau a ce Yemi Osinbajo aka tsaida a matsayin ‘dan takara, amma aka biyewa son kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hirar da DCL Hausa tayi da ita, an ji Naja’atu tana cewa son rai ya jawo aka tsaida Tinubu, amma Osinbajo a matsayinsa na Farfesa, ya fi dacewa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Bauchi Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta saurari tattaunawar da aka yi da wannan Baiwar Allah, an ji tana cewa da gangan Gwamnonin APC masu-ci suka goyi bayan Tinubu.

Naja’atu Mohammed take cewa Gwamnonin su na so ‘dan takaran ya samu mulki ne domin ya danne masu kan maciji, su kuma suyi ta wasa da jelarsa.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Sun soke kudin Tinubu - Naja'atu

“Kwarai, su na karbar kudin da Asiwaju ya ba su, su na rabawa. Wannan abin kunya ne. Ban taba jin labari ko na ga wannan abin ba akalla a zamanin nan.
Na yi shekara da shekaru ina siyasa, a cikin ta aka haife ni. Amma ban taba ganin ‘dan takaran kujerar shugaban kasa yana daukar nauyin Gwamnoni ba.”

- Naja’atu Mohammed

Tsohuwar Darektar kamfen take cewa idan Tinubu ya kashe kudinsa wajen samun takara, hakan yana nufin muddin ya samu mulki, zai dawo da kudinsa ne.

Tinubu ya maidawa Naja' martani

An samu rahoto, Hadimin Bola Tinubu, Mahmud Jega ya ce Naja’atu Mohammed ta sulale daga PCC ne bayan an shirya korarta daga Darekta a kamfe.

A wani jawabi da Mahmud Jega ya fitar, ya ce an gano Naja’atu Mohammed ungulu ce da kan zabuwa, ya ce ‘dan takaran ya yi wa ‘Yan Arewa tanadi.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Bai Samun Goyon Baya da Kyau - Jigon APC Ya yi wa Buhari Gori

Asali: Legit.ng

Online view pixel