A Karshe Gwamna Makinde Ya Kawo Karshen Rikicin PDP, Zai Jagoranci Kamfen Din Atiku a Oyo

A Karshe Gwamna Makinde Ya Kawo Karshen Rikicin PDP, Zai Jagoranci Kamfen Din Atiku a Oyo

  • Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na gab da zuwa karshe gabannin zaben 2023
  • Sabon rahoto ya tabbatar da cewar Gwamna Seyi Makinde, mamba a Kungiyar gwamnonin G-5 ya yarda zai jagoranci gangamin kamfen din Atiku Abubakar a Ibadan
  • Gwamna Makinde da G-5 sun shafe tsawon lokaci yanzu suna adawa da Atiku kan harkokin jam’iyyar

Oyo - Ana sa ran gwamnan Oyo, Seyi Makinde, mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Hakeem Gbolarumi, tsohuwar ministar Abuja, Oloye Jumoke Akinjide za su halarci gangamin kamfen din Atiku Abubakar da za a yi a jihar a ranar Alhamis.

Wannan ci gaban ya kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP reshen jihar, Nigerian Tribune.

Seyi Makinde da Atiku Abubakar
A Karshe Gwamna Makinde Ya Kawo Karshen Rikicin PDP, Zai Jagoranci Kamfen Din Atiku a Oyo Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa za a gabatar da dukkanin yan takarar jam’iyyar a hukumance a wajen taron.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP, Dan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Bar Tafiyar Atiku, Sun Koma Kwankwaso

Gwamna Makinde wanda shine shugaban matasa a kungiyar G-5 ya sha nanata cewa dole ayi abun da ya dace don jam’iyyar ta yi nasara a matakin kasa, musamman a wajen bin tsarin karba-karba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matsayinsa ya yi sanadiyar rabuwar jam’iyyar reshen jihar gida biyu, inda sauran jiga-jigan jam’iyyar a muhawararsu suka bayyana cewa kwamitin NEC ne kadai ke da ikon cire shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ba Atiku ba.

Sai dai kuma, da wannan ci gaban, ana ganin zaman lafiya ya dawo jam’iyyar, kasancewar dukkanin bangarorin sun yarda su ajiye banbancinsu sannan su yi aiki don nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.

Manyan jiga-jigan PDP 8 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Zamfara

A wani labarin, yayin da ake gab da shiga watan babban zaben shugaban kasa a Najeriya, wasu jiga-jigan PDP a jihar Zamfara sun fice daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku da Ayu Sun Ziyarci Magoya Bayan PDP da Hatsarin Mota Ya Ritsa da Su, Sun Ba da Tallafin Miliyan N40

Masu sauya shekar sun da suka koma jam'iyyar APC mai mulki, sun yi takarar kujerar yan majalisar jiha a zaben fidda gwanin PDP da aka yi a shekarar da ta gabata.

Da suke mika takardun tantancewarsu na PDP ga Gwamna Bello Matawalle a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, masu sauya shekar sun ce sun fice daga PDP ne saboda ta rasa alkibla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel