Tsohon Shugaban PDP da Mamban Majalisar Gombe Sun Koma NNPP

Tsohon Shugaban PDP da Mamban Majalisar Gombe Sun Koma NNPP

  • Tsohon shugaban PDP a jihar Gombe tare da dandazon magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Kwankwaso
  • Dan takarar gwamna, Khamisu Mailantarki, shugaban NNPP na jiha da wasu jiga-jigai ne suka halarci bikin tarbansu
  • Mamban majalisar dokoki mai wakilntar mazabar Kaltungo ta yamma ya fita daga APC ya koma mai kayan marmari

Gombe - Tsohon shugaban Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe, Honorabul Shuaibu Baba Sabulu, da dumbin magoya bayansa sun koma jam'iyar NNPP.

Dan takarar gwamnan jihar na NNPP, Alhaji Khamisu Mailantarki, shugaban jam'iya, Maikano Abdullahi, da wasu jiga-jigai ne suka yi maraba da masu sauya shrkar a karamar hukumar Billiri.

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.
Tsohon Shugaban PDP da Mamban Majalisar Gombe Sun Koma NNPP Hoto: leadership
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa a wurin karban tuban tsohon jigon PDP a Billiri, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar, Phillips Bataliya, ya biyo ayari zuwa cikin NNPP.

Kara karanta wannan

Ana Gab da Zabe, Dubbannin Jiga-Jigan APC a Mahaifar Babban Ministan Buhari Sun Koma PDP

Da yake jawabi a wurin taron, Mailantarki ya basu tabbacin cewa za'a tafi da su a dukkan harkokin tafiyar da jam'iyyar musamman yanzu da ake gab da fara kamfe gadan-gadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma roke su da su shiga lungu da sako na jihar Gombe su tara wa jam'iyyar NNPP magoya baya gabanin babban zabe a watan Fabrairu da Maris.

Mailantarki ya kara da cewa ta hanyar haɗa masoya tun daga tushe da kuma wayar da kan masu kaɗa kuri'a ne kaɗai NNPP zata ragargaji jam'iyyar APC mai mulki.

Da yake mika masu katin zama cikakkun mambobin NNPP, Maikano Abdullahi, ya tabbatar masu cewa sun zama ɗaya da kowa kuma za'a basu damarmaki kamar kowa.

Haka nan da yake magana a madadin masu sauya sheka, Baba Sabulu yace sun yanke barin PDP zuwa NNPP ne saboda Gombe na bukatar shugabanci na gari kuma a ganinsu Mailantarki zai iya.

Kara karanta wannan

Saura Yan Makonni Zabe, Atiku da PDP Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Dan majalisa ya koma NNPP

Mamba mai wakiltar mazaɓar Kaltungo ta yamma a majalisar dokokin jihar Gombe, Bashir Yakubu Barau, ya fice daga APC zuwa NNPP ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kafin sauya shekarsa, NNPP da PDP na da yan majalisa uku uku, amma bayan matakin da ya ɗauka a yanzu NNPP na da yan majalisar jiha hudu, wanda ya maida ita babbar jam'iyar adawa.

A wani labarin kuma Jiga-Jigan APC a Mazabar Ministan Buhari Sun Sauya Sheka Zuwa jam'iyyar PDP

Ƙasa da kwana 40 kafin zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, Tinubu ya gamu da cikas a jihar Benuwai.

Dubbannin yan siyasa a mahaifar ministan Ayyuka na musamman a gwamnatin Buhari sun yaga katin APC, Sun ce ba su amfana da komai a matsayinsu na 'ya'yan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel