Atiku, Ayu Sun Ziyarci Wadanda Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Su a Filato, Sun Ba da Gudunmawar Miliyan N40

Atiku, Ayu Sun Ziyarci Wadanda Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Su a Filato, Sun Ba da Gudunmawar Miliyan N40

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga al'ummar jahar Filato
  • Atiku ya jagoranci shugabannin PDP na kasa zuwa asibitin JUTH domin duba mambobin jam'iyyar da hatsarin mota ya cika da su
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar da PDP sun bayar da guduawar naira miliyan 40 ga wadanda abun ya ritsa da su

Plateau - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya bayyana hatsarin da ya lakume rayukan magoyaba bayan jam’iyyar da ke hanyar dawowa daga gangamin kamfen din Atiku/Muftwang a Failato ta tsakiya a matsayin abun takaici.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigan jam’iyyar zuwa jihar don yi wa al’ummar Filato jaje a kan lamarin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Lauya Ya Shawarci Atiku da Gwamnonin G5 Kan Abinda Ya Kamata

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayar da gudunmawar naira miliyan 30 ga wadanda abun ya ritsa da su, AIT ta rahoto.

Atiku da Ayu
Atiku, Ayu Sun Ziyarci Wadanda Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Su a Filato, Sun Ba da Gudunmawar Miliyan N40 Hoto: Atiku Abubakar, PDP
Asali: Facebook

Jam’iyyar PDP reshen Filato da al’ummar jahar na cikin juyayi sakamakon wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyar mutuwar wasu magoya bayan jam’iyyar wadanda ke a hanyarsu ta dawowa daga gangamin kamfen din Atiku Mutfwang wanda aka yi a Pankshin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kan wannan dalili ne dan takarar shugaban kasa na PDP ya datse harkokin kamfen dinsa don kai ziyara da jaje ga mutanen jihar.

Atiku ya fara kai ziyara gidan jigon PDP a jihar kuma tsohon gwamna Jonah Jang, inda ya bayar da gudunmawar naira miliyan 30 ga wadanda abun ya ritsa da su.

Hakazalika, shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 10 ga mutanen a madadin jam’iyyar. Ya ce za dunga tunawa da wadanda abun ya ritsa da su a matsayin jaruman damokradiyya, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Jang wanda ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici ya yi godiya ga Atiku da mukarrabansa kan wannan girmamawar, yana mai cewa PDP a jihar Filato ta fi da hadin kai.

Atiku ya kuma ziyarci wadanda abun ya cika da su a asibitin koyarwa na jami’ar Jos inda ya roki Allah ya ba su lafiya.

Ya kuma ziyarci basaraken Mgwagavul, John Hirse kafin ya bar garin Jos.

APC ta dakatar da harkokin kamfen dinta a Filato don taya PDP jimamin rashin da ta yi

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar APC reshen jahar Filato ta tsayar da lamuran kamfen dinta don taya PDP da mutanen jahar alhinin rashin wadanda suka rasa ransu sakamakon hatsarin mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel