Tsoffin Masu Neman Takara a PDP 8 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Zamfara

Tsoffin Masu Neman Takara a PDP 8 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Zamfara

  • Yan makonni gabanin babban zabe, jam'iyyar APC mai mulki ta samu karin goyon baya a yankin arewa
  • Manyan jiga-jigan PDP wadanda suka yi takara a zaben fidda gwanin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a jihar Zamfara
  • Gwamna Bello Matawalle ya jinjinawa masu sauya shekar kan wannan mataki da suka dauka na komawa cikinsu

Zamfara - Tsoffin masu neman takarar kujerar yan majalisar jaha karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su takwas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara.

A wata sanarwa da sakataren labaran APC a jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya saki a ranar Talata, 17 ga watan Janairu, ya ce tsoffin masu takarar sun sanar da ficewarsu ne a wani taro da suka yi da Gwamna Bello Matawalle a garin Gusau.

Kara karanta wannan

2023: Bidiyon Yadda Aka Ceci Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Tulin Jama'a Ya Fito

Idris ya ce dukkaninsu sun yi takara a zaben fidda gwanin PDP na majalisar dokokin jaha wanda ya gudana a mazabunsu mabanbanta da ke fadin jihar, rahoton The Nation.

PDP da APC
Tsoffin Masu Neman Takara a PDP 8 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewarsa, masu sauya shekar sun hada da Kasimu Jafaru daga mazabar Zurmi ta yamma, Rukkayya Abdullahi daga mazabar Zurmi ta gabas, Isah Ibrahim-Labbo daga mazabar Anka da Abubakar Abdulaziz, daga mazabar Tsafe ta gabas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran masu sauya shekar sune Bala Ibrahim da Jamilu Bawa daga mazabar Birnin Magaji, Ibrahim Surajo daga Zurmi ta yamma da jagoran tawagar masu sauya shekar, Murtala Mainasara daga mazabar Shinkafi.

Ya ce masu sauya shekar wanda shugaban APC a jihar, Alhaji Tukur Danfulani, ya gabatar da su ga gwamnan, sun mikawa Matawalle dukkanin takardunsu na PDP.

PDP ba ta da alkibla shiyasa muka koma APC, Mainasara

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

Idris ya nakalto Mainasara yana cewa:

"Mun yanke shawarar komawa APC ne saboda rashin alkibla a PDP.
"Mun dawo APC ne saboda tsarin shugabancin gwamna Matawalle da kuma yadda ya mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da sauya fasalin tattalin arzikin jihar."

Yayin da yake tarbarsu, Idris ya nakalto Matawalle na cewa masu sauya shekar APC jam'iyya ce ta duk wasu masu tunani da yan Najeriya masu kishin kasa da suka mayar da hankali kan ci gaba.

Idris ya ce:

"Gwamnan ya jinjina masu kan abun da ya kira da shawara mai kyau na komawa APC.
"Matawalle ya ce bai ji mamaki kan shawararsu ba duba ga irin kokarin da suke yi na kawo ci gaba ga masu zabe."

Da farko, yayin da yake gabatar da masu sauya shekar ga gwamnan, Danfulani ya ce akwai karin yan PDP da za su dawo APC a kwanaki masu zuwa, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ta Lanjarewa Tinubu a Arewa, 'Ya'yan APC 20,350 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

APC ta rasa dubban mambobinta a Bauchi, sun koma PDP

A wani labarin makamancin wannan, mun ji cewa mambobin APC sama da 20,000 sun fice zuwa PDP a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel