Rikicin Gidan da Ya Kunno Zai Kawo Cikas, An Zargi Jigo a PDP da Munafuntar Atiku

Rikicin Gidan da Ya Kunno Zai Kawo Cikas, An Zargi Jigo a PDP da Munafuntar Atiku

  • Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a Imo ya samu rashin jituwa da Emeka Ihedioha
  • Shugaban kwamitin PCC na reshen Imo yana zargin ba da gaske Ihedioha yake tare da Atiku ba
  • Mai magana da yawun PDP a jihar, Collins Okpuruzo ya kare tsohon Gwamnan daga zargin yaudara

Imo - Akwai sabani a jam’iyyar PDP ta reshen jihar Imo tsakanin tsohon Gwamna watau Emeka Ihedioha da kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa.

Vanguard ta ce rigimar da ake yi tsakanin bangaren Hon. Emeka Ihedioha da kwamitin neman takarar Atiku Abubakar a zaben 2023 ya yi kamari yanzu.

Greg Egu wanda shi ne Darekta Janar na PCC a jihar Imo, yana zargin Emeka Ihedioha da kawo masu matsala a yakin neman zaben Atiku da Okowa.

Egu yake cewa Ihedioha ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya hana kwamitinsa da ke yi wa Atiku Abubakar kamfe a jihar Imo tallata su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Jagororin APC Sun Gaza Nunawa Tinubu Kara, Sun Kunyata Shi Wajen Yakin Zabe

An samu nakasu a tafiyar Atiku

‘Dan siyasar ya shaidawa manema labarai a garin Owerri cewa abubuwan da Ihedioha ya tsiro da su, za su iya gurgunta yakin neman zaben Atiku sosai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Egu, duka ‘yan takara 41 da PDP take da su a Imo sun gagara yi wa Atiku kamfe saboda yadda tsohon Gwamnan jihar yake tafiyar da abubuwansa.

Atiku
Yakin zaben PDP a Imo Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Ungulu ne da kan zabo?

Rahoton ya ce ana zargin tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyar da zama ungulu da kan zabo a PDP, an ce mutanensa sun kauracewa duka taron PCC a Imo.

Darekta Janar din yakin zaben ya ce babu ta yadda mutum zai rika tallata Atiku, a gefe guda kuma yana kokarin kashewa kwamitin yakin zabensa kasuwa.

Ba komai ya jawo Ihedioha yake yin haka ba sai saboda yana burin sake zama Gwamna, wannan shi ne ra’ayin Greg Egu wanda ya ce dole a dauki mataki.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bude Baki Ya Saki Maganganu, Ya Fadi Yadda Atiku Ya Samu Takara a PDP

People Gazette ta kawo rahoto cewa sabanin Samuel Anyawu da Ihedioha wanda kotu ta tunbuke daga kujerar Gwamna ya kara dagula halin da PDP ke ciki.

Kakakin jam’iyyar hamayyar a jihar Imo, Collins Okpuruzo ya musanya zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan, ya wanke shi daga tuhumar juyawa Atiku baya.

Tinubu zai doke Atiku - 'Dan majalisa

An ji labari cewa Hon. Shamsudeen Danbazzau wanda ya yi ‘yan kwanaki a NNPP kafin dawowa APC ya fadi abin da zai nakasa Atiku Abubakar a zaben bana.

‘Dan majalisar wakilan tarayyar yake cewa Bola Tinubu zai doke ‘yan takaran 2023 a saukake, domin yana gefe guda 'yan takaran LP da NNPP za suyi masa aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel