Jagororin APC Sun Gaza Nunawa Tinubu Kara, Sun Kunyata Shi Wajen Yakin Zabe

Jagororin APC Sun Gaza Nunawa Tinubu Kara, Sun Kunyata Shi Wajen Yakin Zabe

  • Jiga-jigan APC na Enugu da-dama ba su iya zuwa wajen taron yakin neman zaben Bola Tinubu ba
  • Irinsu Sullivan Chime, Geoffrey Onyeama, da Sanata Ken Nnamani sun kaurcewa taron jam’iyyarsu
  • Hakan ya faru a dalilin sabanin da ake da shi da Shugaban APC na jihar, Ugochukwu Agballah

Enugu - Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta reshen jihar Enugu, ba su halarci taron yakin neman zaben Bola Tinubu da aka shirya ba.

Daily Trust ta fahimci cewa da farko dai kusoshin jam’iyyar APC sun yi wa Asiwaju Bola Tinubu a filin tashin jirgin sama Akanu Ibiam da ke garin Enugu.

Bayan nan kuma sai aka nemi jiga-jigan jam’iyyar a wajen taron kamfen ‘dan takarar, aka rasa.

Wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC da suka kauracewa taron yakin zaben sun kunshi Ministan harkar kasar waje, Geoffrey Onyeama da Sanata Ken Nnamani.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da ‘Yan Kwamitinsa, APC Ta Fara Shiga Kawance da Wasu Jam'iyyu

Baya ga tsohon shugaban majalisar dattawan, tsohon Gwamna, Sullivan Chime da tsohon shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon. Eugene Odo, sun ki zuwa.

Fushi ake yi da Bola Tinubu?

Vanguard ta rahoto Sullivan Chime yana fadawa ‘yan jarida cewa sun tarbi ‘dan takarar a filin jirgi, amma ba za su samu zuwa inda yake taron kamfe ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jagororin APC
Taron Yakin Zaben APC a Enugu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Enugu ya ce sun dauki wannan mataki ne a sakamakon sabaninsu da shugaban APC na reshen jihar, Cif Ugochukwu Agballah.

‘Dan siyasar yake cewa idan za a tuna sun yi zanga-zanga a sakatariyar jam’iyya da ke Abuja a game da mummunar dabi’ar Agballah, amma ba ayi komai ba.

Chime da mutanensa su na zargin cewa babu wanda ya san Agballa a siyasar Enugu, kuma tun da suka zama shugabannin jam’iyya, APC ta wargaje a Enugu.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Kasa, da 'Yan APC 4 da Ba a Taba Gani Wajen Yakin Zabe ba

Ana kukan ‘dan takarar gwamnan da mataimakinsa sun fito daga yanki daya. Punch ta ce 'yan siyasar sun nuna a shirye suke da su yi wa Bola Tinubu aiki.

Kira ga shugabannin APC

A jawabinsa, Hon. Eugene Odo ya ce babu wani babba a jam’iyyar APC ta Enugu da ya halarci gangamin Tinubu a dalilin rikicin da ake yi da su Cif Agballah.

Tsohon shugaban majalisar dokokin ya yi kira ga Hope Uzodinma a matsayinsa na jagoran APC a Kudu maso gabas, da ya tabbatar an yi adalci a jam’iyyar.

Gwamna Wike da rikicin PDP

Rahoto ya nuna har yau Gwamnan Ribas, Nyesom Wike bai hakura da abin da ya faru a zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasan 2023 na jam'iyyar PDP ba.

Da ya gama bambaninsa, an ji Wike ya tona asirin yadda ‘yan siyasa ke neman amfani da kudi a zabe mai zuwa, ya ce akwai badakala a kasafin NDDC.

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku: An Tona Sunan Dan Takarar da Kwankwaso da Peter Obi Suke Wa Aiki a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel