Wike Ya Bude Baki Ya Saki Maganganu, Ya Fadi Yadda Atiku Ya Samu Takara a PDP

Wike Ya Bude Baki Ya Saki Maganganu, Ya Fadi Yadda Atiku Ya Samu Takara a PDP

  • Nyesom Wike ya samu sabani da shugabannin Jam’iyyar PDP, har ya bukaci a tunbuke Iyorchi Ayu
  • Gwamnan Jihar Ribas yana zargin PDP ta saba doka a wajen zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa
  • Wike yace kaunar da ke tsakaninsa da Jam’iyyar PDP ta hana shi kalubalantar nasarar Atiku Abubakar

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda abubuwa suke gudana a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Gwamnan ya yi magana ne a lokacin da shugabannin gidan jaridar kamfanin The Sun Publishing Limited suka gabatar masa da wasikar lambar yabo.

Mai girma Nyesom Wike ya sake nanata cewa an saba doka a wajen zaben tsaida gwanin da ya ba Atiku Abubakar damar samun tikitin jam’iyyar PDP.

A cewar Nyesom Wike, zaben tsaida ‘dan takaran PDP cike yake da abubuwan da ba su dace ba, amma bai iya yin bayanin yadda aka sabawa dokoki ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: Bana goyon bayan Atiku, ba kuma zan tursasawa 'yan jiha ta su bi ra'ayi na ba

Meya hana Wike zuwa Kotu?

Gwamnan na Ribas ya ce in ban da soyayyar da yake yi wa jam’iyyar PDP, da ya shiga da kara a kotu domin ya kalubalanci sakamakon zaben da aka shirya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta Sun ta rahoto Gwamnan yana cewa babu wani huro wuta da za a iya yi masa domin a rufe masa baki har ya daina fadin abin da yake gaskiya.

Takara a PDP
Taron yakin zaben PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Badakala a kasafin kudin NDDC

Da yake magana, Gwamna Wike ya ankarar da al’umma a game da kasafin kudi N500bn na hukumar NDDC da aka dage sai majalisa ta amince da shi.

Wike mai barin gadon mulki a Mayu ya ce cuwa-cuwa ce a kasafin kudin NDDC, ya ce ‘yan siyasa na neman hanyar samun kudin da za a kashe wajen zabe.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Tsohon Ministan tarayyar ya zargi ma’aikatan wannan hukuma da ke kula da harkokin Neja-Delta da cin amanar mutane a maimakon suyi ayyuka.

Daga cikin zargin da Wike yake yi wa hukumar shi ne an ware N4bn da sunan za a gyara kwatoci a jihohin da ke Neja-Delta alhali gwamnoni ba su sani ba.

Wike ya ji dadin lambar yabo

A karshe, Wike ya godewa The Sun Publishing Limited da aka ba shi wannan kyauta na shekarar 2022, ya kuma yi kira cewa su maida hankali a aikunsu.

An karrama jigon na PDP ne da lambar yabo na zama jajirtacce wajen shugabanci.

Da sauran aiki - Tinubu

Rahotonmu ya nuna Bola Tinubu mai takarar shugabancin Najeriya a APC ya fitar da jawabin da yake nuna akasin abin da Muhammadu Buhari ya fada.

‘Dan takaran yana gani ba a gama shawo-kan matsalar tsaro ba, sannan ya fadi yadda zai magance yajin-aikin ASUU da ya gagari gwamnati mai-ci.

Kara karanta wannan

2023: An Yi wa Atiku Iyaka Wajen Neman Mulki, An hana Shi Yin Kamfe a Jihar PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel