Abin da Gwamna Ya Fada a Kan Kwankwaso da ya Ziyarci Jihar Abokin Hamayyarsa

Abin da Gwamna Ya Fada a Kan Kwankwaso da ya Ziyarci Jihar Abokin Hamayyarsa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Gwamna Charles Chukwuma Soludo a gidan Gwamnati da ke Awka
  • Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya karbi Kwankwaso da mutanensa da kyau, ya yi masu fatan alheri
  • ‘Dan takaran na jam’iyyar NNPP ya je jihar Anambra domin a bude wasu ofisoshin yakin neman takara

Anambra - Farfesa Charles Chukwuma Soludo wanda shi ne Gwamnan jihar Anambra, ya ce Najeriya na bukatar shugabannin da suka yi imani da kasar.

The Cable ta ce Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karbi bukuncin Rabiu Musa Kwankwaso a gidan gwamnatin jihar Anambra.

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso da ‘yan tawagarsa sun kai wa Gwamnan ziyara yayin da suka je kaddamar da ofisoshi.

Da yake bayani a ranar Alhamis, 5 ga watan Junairu 2023, Farfesa Chukwuma Soludo ya ce bai dace neman kujerar siyasa ta zama wani abin a-mutu-ko ayi rai ba.

Kara karanta wannan

2023: Magana Ta Kare, Wike da Ortom Sun Hada Baki, Sun Yi Magana Kan Dan Takarar da G5 Zata Marawa Baya

Akwai alamun nasara nan gaba - Soludo

Mai girma Gwamnan yake cewa duk da halin da ake ciki a yau, Najeriya ta na da damar da tattalin arzikinta zai shiga sahun wadanda suke kan gaba a Duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin Christian Aburime ya nuna Mai gidanta, Gwamna Soludo ya jinjinawa Kwankwaso, ya ce ya bar misali a aikin gwamnati da yadda ya damu da kasar.

Kwankwaso
Magoya bayan NNPP a Awka Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kowa ya zabi wanda yake so a Anambra

A cewar Gwamnan, a jihar Anambra – mahaifar irinsu Azikiwe, Akweke, Chinua Achebe, Okadigbo, mutane su na da damar da za su zabi duk wanda suke so.

Ibo su na cewa ‘Oje mba, enwe ilo’, hakan yana nufin a ba kowa ‘yanci ya yi zabin da ya ga dama.

A karshe, tsohon gwamnan na bankin CBN ya yi wa Kwankwaso fatan alheri a takarar da yake yi, duk da sabanin da ke tsakanin jam’iyyarsa ta APGA da NNPP.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Kayan marmari sun je kasar Ibo

VON ta ce ‘dan takaran shugaban kasar na NNPP ya kaddamar da ofisoshin jam’iyya mai alamar kayan dadi yayin da ya kai ziyara zuwa yankin Kudu maso gabas.

Kwankwaso wanda ya yi Gwamna a jihar Kano ya ce sun yi nasarar shigar da jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa duk wani lungu da sako domin a ceto al’umma.

Obasanjo mutumin kirki ne? - Tinubu

Da ya je jihar Edo domin ya yi kamfe a makon nan, an ji labarin yadda Asiwaju Bola Tinubu ya caccaki Olusegun Obasanjo a kan goyon bayan Peter Obi.

Bola Tinubu ya ce ayi hattara da tsohon Shugaban kasar na Najeriya domin duk ‘dan takaran da Cif Olusegun Obasanjo ya tsaida a zabe, guba ne a gare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel