NNPP Ta Cigaba da Yi wa PDP Dauki Daya-Daya, Ta Dauke Jigon Adawa a jihar Arewa

NNPP Ta Cigaba da Yi wa PDP Dauki Daya-Daya, Ta Dauke Jigon Adawa a jihar Arewa

  • Mahmud Mohammed Wafa ya sauya-sheka daga Jam’iyyar adawa ta PDP zuwa NNPP mai kayan dadi
  • Kafin barinsa PDP, Mahmud Mohammed Wafa shi ne Mai binciken kudi na jam’iyyar PDP a Gombe
  • ‘Dan siyasar ya soki Gwamnatin APC da ke mulki, sannan ya ce jam’iyyar PDP ba za ta iya ceto jihar ba

Gombe - Babban mai binciken kudi na jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Mahmud Mohammed Wafa ya sauya-sheka zuwa NNPP mai alamar kayan dadi.

Leadership ta rahoto cewa Mr. Mahmud Mohammed Wafa ya sanar da ficewarsa daga PDP ne da ya zanta da manema labarai a cikin farkon makon nan.

Hakan na zuwa ne bayan ya yi zama da ‘dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Hon. Khamis Ahmed Mailantarki.

Kara karanta wannan

Tinubu zai tashi a tutar babu: Dan takarar gwamna a Arewa ya bar APC, ya shige inuwar PDP

Mahmud Mohammed Wafa ya ce ya bar PDP ne ya shigo tafiyar Khamis Ahmed Mailantarki a NNPP ne domin a ceci jihar daga gwamnati mai mulki.

Jam'iyyar PDP ba za ta iya ba

‘Dan siyasar yake cewa a halin da ake tafiya a kasar, jam’iyyar PDP ba za ta iya kawo canjin da ake bukata ba a dalilin rikicin gidan da take fama da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NNPP.
Jagororin NNPP a Gombe Hoto: Kwankwason Twitter, @baba
Asali: Twitter

Duba da mummunan halin da ake ciki yanzu, mu na bukatar a zauna a hada-kai domin a ceto jihar a hannun gwamnatin APC mai mulki.

Kuma PDP ta balbalace kuma ta shiga rudani tun bayan zaben tsaida gwani a watan Maris, ba za su iya ba mu jagorancin da muke so ba.

Shakka babu da irin ayyukan da ya yi a baya da kan-kan da kan shi, Mailantarki zai jagoranci jihar nan fiye da ‘ya ‘yan APC da kuma PDP.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

Jam’iyyar NNPP ce kurum turbar da za mu bi wajen daidaita jihar nan bayan 2023.

PDP ta na ta yin asara a Gombe

Jaridar Sun ta rahoto Muhammad Wafa yana cewa gwamnatin APC ta jefa Gombe a cikin hadari, yake cewa mutanen jihar sun shiga halin ha’ula’i.

Ba Wafa ne shugaba na farko a jam’iyyar PDP da ya sauya-sheka ba. Kwanaki wasu jagororin PDP a karamar hukumar Funakaye suka shiga NNPP.

APC za ta lashe Yobe

An rahoto Mataimakin Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Idi Gubana a madadin Gwamna Mai Mala Buni ya ba Bola Tinubu 99.9% na kuri’un da za a kada.

Idan dai aka tafi a haka, manyan ‘yan takaran shugabancin kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar da Rabiu Kwakwaso ba za su tsira da komai a Yobe ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel