Atiku Zai Tashi a Tutar Babu, Gwamnan Arewa Ya yi wa APC Alkawarin 99.9% na Kuri’unsa

Atiku Zai Tashi a Tutar Babu, Gwamnan Arewa Ya yi wa APC Alkawarin 99.9% na Kuri’unsa

  • Mafi yawa ko kusan duka mutanen jihar Yobe za su ba Asiwaju Bola Tinubu kuri’arsu a zaben 2023
  • Wannan shi ne alkawarin da Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa wasu magoya bayan ‘dan takaran APC
  • Buni yana sa rai Bola Tinubu ya tashi da kashi 99.9% na kuri’un Yobe a zaben shugabancin Najeriya

Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi alwashin cewa kashi 99.9% na kuri’un mutanen Yobe za su tafi ne wajen Asiwaju Bola Tinubu.

Vanguard ta rahoto Mai girma Mai Mala Buni yana cewa Asiwaju Bola Tinubu zai yi nasara a Yobe a zaben da za ayi a watan Fubrairun nan mai zuwa.

Mala Buni ya yi wannan alkawari lokacin da ya karbi bukuncin kwamitin wasu mutane masu zaman kansu da ke yi wa Tinubu/Shettima kamfe.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Musanya Rade-Radin Fama da Cuta, Ya Fadi Abin da ke Nuna Koshin Lafiyarsa

'Yan kwamitin ICC sun dage da kamfe

A wajen taron aka ji Gwamnan yana cewa jam’iyyar APC ta samu karbuwa sosai a jihar Yobe a dalilin ayyukan cigaba da more rayuwa da ya kawo.

Mataimakin Gwamnan Yobe, Alhaji Idi Gubana ya wakilci Buni wajen tattaunawarsa da ‘yan kwamitin na ICC a ranar Talatar nan a garin Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya fadawa kwamitin yakin neman takaran su cigaba da kokarin da suke yi na ganin sun hada kan duk kungiyoyin da ke goyon bayan APC.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe a Kaduna Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Buni ya yi masu alkawarin za su dage wajen ganin cewa Bola Tinubu ya karbi shugabancin Najeriya daga hannun Muhammadu Buhari a Mayu.

Shawarar da Buni ya ba kwamitin

“Ku gujewa duk wani nuna bambamci a wajen goyon baya da kokarin tallata Tinubu da Kashim, tare da yin biyayya ga doka wajen yawon yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku? Tsohon Gwamna Musulmi Ya Faɗi Wanda Allah Yace Zai Zama Shugaban Kasa a 2023

An rahoto tsohon Sakataren jam’iyyar APC na kasan yana kira ga masu goyon bayan ‘dan takaran na su, da su zama masu bin doka ko da bayan zaben bana.

Mataimakin shugaban kungiyar ICC na shiyyar Arewa, Umar Ibrahim ya bayyana cewa su na kokarin ganin sun hada-kan kungiyoyin magoya bayan APC.

Pulse ta rahoto Alhaji Umar Ibrahim ya ce za suyi abin da zai kawowa kasar nan cigaba.

Zan cire tallafi - Tinubu

Idan aka zabe shi ya zama Shugaban Najeriya, an ji labari cewa Bola Tinubu ya sha alwashin cire tallafin man fetur duk da hakan zai jawo karin farashi.

‘Dan Takaran APC na zaben 2023 ya ce tsarin tallafin mai bai amfanar talaka don haka zai karkatar da kudin wajen yin abubuwan da za su amfani kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel