2023: Gwamnonin G-5 Ba Zasu Fice Daga Jam'iyar PDP Ba, Walid Jibrin

2023: Gwamnonin G-5 Ba Zasu Fice Daga Jam'iyar PDP Ba, Walid Jibrin

  • Tsohon shugaban BoT na jam'iyyar PDP yace babu daya daga cikin gwamnonin G5 da zai sauya sheka zuwa wata jam'iya
  • Sanata Walid Jibrin ya musanta jita-jitar cewa matsin lambar tawagar Wike ce ta sa ya yi murabus daga mukaminsa
  • Ana ta kai ruwa rana a jam'iyyar PDP kan batun raba manyan mukamai na kasa tsakanin kudu da arewa

Nasarawa - Tsohon shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar PDP ta kasa, Sanata Walid Jibrin, ya bayyana cewa gwamnonin G-5 ba zasu watsar da jam'iyarsu ba duk da sabanin da aka samu.

Jibrin ya kuma tabbatar da cewa duk wannan kurar dake tashi a cikin PDP zata zama tarihi kafin ranar zabe a wata mai zuwa, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Sanata Walid Jibrin.
2023: Gwamnonin G-5 Ba Zasu Fice Daga Jam'iyar PDP Ba, Walid Jibrin Hoto: vanguard
Asali: Depositphotos

A cewar Sanata Jibril, duba da kusancinsa da tawagar da kuma kishin haɗin kan jam'iyya, yana da kwarin guiwar cewa abokansa watau mambobin G5 zasu yi wa PDP aiki da kishin kasa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

Shin dagaske rigimar G5 ta sa ya yi murabus?

Tsohon shugaban BoT ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a garin Marmara dake jihar Nasarawa ranar Laraba 4 ga watan Disamba, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babban Jigon ya kuma musanta rade-radin cewa ya yi murabus daga shugaban BoT-PDP ne saboda matsin lambar G-5, inda yace batu ne na fahimtar juna.

A kalamansa, Sanata Walid Jibril ya ce:

"Gwamnonin G5 na gwada 'yan Najeriya ne kawai, nan ba da jimawa ba zasu sasanta saboda sun shirya dawo da fatan 'yan Najeriya waɗanda mulkin APC ya jefa su cikin tsadar rayuwa."
"Kafin sauka na daga shugaban BoT, na san an lalubo hanyoyin da zasu iya bulle wa kuma na san har yau ana neman bakin zaren domin sulhunta bangarorin biyu, batun na da sauki."

Shin G5 zasu iya barin PDP kafin zabe?

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin PDP Biyu Sun Ziyarci Abokin Gamin Atiku, Sun Fadi Abinda Suke Fatan A Yi Wa Su Wike G5

Tsohon shugabam BoT ya kara tabbatar da cewa wannan sabanin da ake gani a PDP tsakanin tsagi guda biyu zai zo karshe cikin nasara.

"Ba inda G5 zasu tafi suna nan tare da mu a PDP, muna kallonsu da duk abinda suke aikatawa, abin zai baku sha'awa idan kuka gano gwada yan Najeriya kawai suke yi."

A wani labarin kuma Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa

Ga dukkan alamu kalaman gwamna Wike game da zaben shugaban kasan 2023 bai wa makusantan Atiku dadi ba, an ci sun fara guna-guni da maida martani.

Phrank Shaibu ya ce ba zai yuwu Wike ya ba da labarin abinda ya faru a wancan lokacin ba domin bai san komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel