Kwamitin Zaben Bola Tinubu Ya Rabawa Kiristoci Buhunan Abinci 1, 000 a Arewa

Kwamitin Zaben Bola Tinubu Ya Rabawa Kiristoci Buhunan Abinci 1, 000 a Arewa

  • Jam’iyyar APC da kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu sun raba buhunan abinci a Zamfara
  • Sanata Kabiru Marafa ya bada kyautar buhunan shinkafa da na masara ga kiristocin jihar Zamfara
  • An raba abincin ne domin kiristocin da ke jihar su ji dadin kirismeti, su kuma zabi 'Yan takaran APC

Zamfara - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Zamfara da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PCC, sun rabawa jama’a tulin buhuna na kayan abinci.

Rahoton Sun na ranar Talata, 3 ga watan Junairu 2023, ya tabbatar da cewa an raba buhuna 1, 000 na shinkafa da garin masara ga kiristocin da ke Zamfara.

An yi rabon kayan abincin ne domin kiristocin jihar su ji dadin bikin kirismeti da sabuwar shekara.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a Zamfara, Yusuf Idris ya fitar da jawabi a farkon makon nan, ya na bayani a kan rabon kayan abincin da aka yi.

Kara karanta wannan

Sabuwar Shekara: Gwamna El-Rufai Ya Yi Wa Fursunoni 3911 Afuwa, Ya Taka Rawar Buga

Jawabin da jam'iyyar APC ta fitar

"Kayan abincin sun kunshi buhuna 250 na shinkafa da buhuna 750 na garin masara da shugaban kwamitin PCC na jihar, Sanata Kabiru Marafa ya rabawa kiristoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wannan ne yayin da aka shiga garuruwan kiristoci domin taya su murnar shiga sabuwar shekara wanda Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya jagoranta.
Marafa ya yi kira ga wadanda suka amfana da kayan da jagoririn kiristoci a jihar su tabbatar wajen ganin mafi yawan mutanensu musamman masu bukata sun amfana."

- Yusuf Idris

Kwamitin Zaben Bola Tinubu
Gwamnan Zamfara tare da Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

This Day ta rahoto Yusuf Idris yana cewa shugaban kwamitin na yakin neman zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima ya tallata ‘yan takaran APC a taron.

Kabiru Marafa ya yi kira ga mutanen da su goyi bayan Bola Tinubu ya zama shugaban kasa.

Ayi wa Najeriya addu'a - Marafa

Kara karanta wannan

2023: Ta Karewa Atiku, Darakta Janar Na Kwamitin Kamfen PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Tsohon Sanatan na Zamfara ta tsakiya, ya bukaci kiristocin da su cigaba da yi wa Najeriya addu’ar samun cigaba, zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro.

Shugaban CAN na reshen Zamfara, Ahmad Haruna da Eze-Igbo na jihar, Igwe Egbuna Obijiaku sun ji dadin irin alherin da ‘yan siyasar suka yi wa mutanensu.

Haruna da Obijiaku sun yi alkawarin za su raba kayan ga wadanda suke da bukata, sannan suka ce za su cigaba da yin addu’a domin ganin an zauna lafiya.

An nada Kwamitin takarar NNPP

A bangare guda, an ji labari Sakararen jam’iyyar NNPP na Najeriya, Dipo Olayoku ya fitar da sanarwar nadin kwamitin da zai yi wa Rabiu Kwankwaso yakin zabe.

Mun fahimci cewa kwamitin na PCC yana kunshe da mutane da-dama, za a rantsar da ‘yan kwamitin kamfen ne a ranar Litinin 9 ga watan Junairu 2022 a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel